Majalisar Tarayya ta amince da kudirin cire ka’idojin shekarun mai neman aiki

Majalisar Tarayya ta amince da kudirin cire ka’idojin shekarun mai neman aiki

A ranar Laraba, 7 ga watan Nuwamba ne majalisar wakilai ta nuna goyon bayanta akan kudirin soke adadin yawan shekarun mai neman aiki, don sake duba kudirin a karo na biyu.

Hakan na nufin cewa an kusa share hawayen masu neman aiki a ma’aikatun tarayya wanda yawan shekaru kan zame masu kalubale, wato za’a daina nuna banbancin shekaru wajen kwasar ma’aikata.

Dan Majalisar Tarayya Sergius Ogun na APC daga jihar Edo neda kuma Babajimi Benson, dan APC daga Lagas ne suka gabatar da kudirin, inda suka nemi cewa takaita yawan shekarun wanda za a dauka aiki a gwamnati na kawo kalunbale matuka a fadin kasar.

Majalisar Tarayya ta amince da kudirin cire ka’idojin shekarun mai neman aiki
Majalisar Tarayya ta amince da kudirin cire ka’idojin shekarun mai neman aiki
Asali: Depositphotos

Ogun ya ce idan aka yarda da wannan doka, za a daina daukar aiki ko kuma kin daukar mutum aiki saboda shekarun sa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Oshiomhole na a hanyar dawowa Najeriya

A Najeriya ana kin daukar mutum aiki komai kwarewar sa idan adadin shekarun sa bai kai na wanda ake so a dauka ba, ko kuma shekarun sa sun haura na wanda ake so a dauka, duk kuwa da irin kwarewar sa ko basirar sa.

Ya ce dokar za ta fara aiki ne a kan hukumomin gwamnatin tarayya kafin sauran sassan ma’aikatu.

Ya kuma jadadda cewa hakan ne kawai zai iya magance yawaitar rashin aiki da matasa da sauran jama’a ke fama da ita a kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel