An gurfanar da jami'in rundunar 'yan sanda da ake zargin ya kashe Miss Anita Akapson

An gurfanar da jami'in rundunar 'yan sanda da ake zargin ya kashe Miss Anita Akapson

- An gurfanar da mataimakin Sufuritandan runduanar a gaban kotu, wanda ake zarginsa da kashe 'yar uwar tsohon sanatan Kudi, Sanata Nenadi Usman

- Bayan da aka karanta karar gaban kotun, wanda ake zargin ya musanya aikata wannan laifi da ake zarginsa da aikatawa

- Bayan sauraron jawabai daga kowanne bangare, mai shari'a A. O. Ebong ya bayar da belin wanda ake zargin akan kudi N50m tare da gabatar da wakilai guda biyu

Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da wani mataimakin Sufuritandan runduanar wanda ake zarginsa da kashe 'yar uwar tsohuwar ministar Kudi, Sanata Nenadi Usman.

A wata takardar tuhumar aikata laifin ta'addanci da aka gabatar gaban babbar kotun gwamnatin tarayya da ke da zama a Zuba, ana zargin Inagozie Godwin, mai shekaru 36 da haihuwa, da harbe Miss Anita Akapson har lahira a yankin Katampe a Abuja, da misalin karfe 9:45pm, na ranar 13 ga watan Oktoba, 2018.

Zargin aikata laifin, wanda jami'i mai shigar da kara ya ce laifin ta'addanci ne, wanda kuma ya ci karo da sashe na 22 sakin layi na (3) na dokar laifi, da hukuncinsa a karkashin sashe na 22 sakin layi na (4) na dokar.

KARANTA WANNAN: Majalisar wakilai za ta binciki badakalar da jam'iyyu suka yi a zabukan fitar da gwani

Miss Anita Akapson

Miss Anita Akapson
Source: Twitter

Bayan da aka karanta karar gaban kotun, wanda ake zargin ya musanya aikata wannan laifi da ake zarginsa da aikatawa.

Jami'i mai shigar da karar, Mr. Donatus Abah, ya bukaci kotu da ta sanya ranar da za a fara sauraron tuhumar don yanke hukuncin da ya dace.

Sai dai, lauya mai kare wanda ake karar, Mr, Paul Samson, ya shaidawa kotun cewa ya gabatar da takardar bukatar belin wanda yake karewa tun a ranar 30 ga watan Oktoba.

KARANTA WANNAN: An gurfanar da magidanci bisa gazawarsa na gabatar da matarsa da ta damfari banki N180m

Bayan sauraron jawabai daga kowanne bangare, kan wannan takarar bukatar belin, mai shari'a A. O. Ebong ya bayar da belin wanda ake zargin akan kudi N50m tare da gabatar da wakilai guda biyu.

Mai shari'a Ebongnya ce ya bayar da belin wanda ake zargin ne sakamakon gazawar jami'i mai shigar da karar na gabatarwa kotu kwararan hujjoji na dalilan da za su sanya kotun ta yi watsi da baiwa DSP Inagozie beli.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel