Amurka, Faransa sun nuna sha'awarsu kan Nigeria Air - Gwamnatin tarayya

Amurka, Faransa sun nuna sha'awarsu kan Nigeria Air - Gwamnatin tarayya

- A ranar Alhamis, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa gwamnatocin kasashen Amurka da Faransa, sun nuna sha'awarsu kan jirgin Nigeria Air

- A hannu daya kuma gwamnatin tarayyar ta karyata rahoton cewa an dakatar da shirin sake samar da jirgin Nigeria Air saboda rashin masu zuba hannun jari

- Ta ce akalla ana bukatar farawa da jarin $55m, inda za ayi amfani da $25m wajen sayen jirgi da kuma $30m a matsayin kudaden gudanarwa

A ranar Alhamis, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa gwamnatocin kasashen Amurka da Faransa, sun nuna sha'awarsu kan jirgin Nigeria Air. A hannu daya kuma gwamnatin tarayyar ta karyata rahoton cewa an dakatar da shirin sake samar da jirgin Nigeria Air saboda rashin masu zuba hannun jari.

Da ya ke jawabi a wani taro na masu ruwa da tsaki kan harkokin sufurin jiragen sama a Abuja, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya kuma bayyana cewa an dakatar da shirin sake farfado da aikin Nigeria Air ne sakamakon gazawar kamfanin da zai bayar da shawara kan gudanarwa, Lufthansa, na bayar da bayanai kan tsarin sanya hannun jari da kuma tabbatar da tsoma 'yan kasuwa a ciki.

Ya ce an cire kamfanin Lufthansa daga tsarin shirin sakamakon bukatun da ya gabatar wadanda ke nuni da bude wasu asusu na daban, da kuma kin biyan kudaden haraji da ma bukatar kaso 75 na kudaden aiki a nan take.

KARANTA WANNAN: Majalisar dattijai za ta amince da dokar sake fasalin rundunar 'yan sanda nan da mako 2

Amurka, Faransa sun nuna sha'awarsu kan Nigeria Air - Gwamnatin tarayya
Amurka, Faransa sun nuna sha'awarsu kan Nigeria Air - Gwamnatin tarayya
Asali: Twitter

Ministan ya zayyana sunyayen masu saka hannun jari da a kullum suke cikin zawarcin jirgin na Nigeria Air da suka hada da bankin bunkasa Afrika ADB, bankin bunkasa Musulunci IDB, gwamnatocin kasashen Amurka da Faransa, da dai sauransu.

Sirika ya ce: "Akwai labaran karya da ake yadawa na dalilan da suka sanya aka dakatar da shirin farfado da Nigeria Air, wasu na ganin cewa rashin masu saka hannun jari ne, wannan kuma ba gaskiya bane.

"A yanzu haka akwai IDB, AfDB, AFREXIM, US-EXIM, bankin Standard Chartered, Boeing, Airbus, COMAC/CCECC, BOAD, China-Exim, Kamfanin sufuri na Qatar, kamfanin sufuri na Ethiopia, da ma asusun bunkasa manyan ayyuka na kasar Deutche, duk sun nuna sha'awarsu, kuma a shirye suke su zuba hannu jari."

Ya ce akalla ana bukatar $300m har zuwa shekarar 2020 don daukar nauyin kamfanin jirgin na Nigeria Air, kuma akalla ana bukatar farawa da jarin $55m, inda za ayi amfani da $25m wajen sayen jirgi da kuma $30m a matsayin kudaden gudanarwa, daga watan Yuni zuwa Disambar 2018.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel