Auren wuri: Wayar wa mata kai ne mafita – Aisha Buhari

Auren wuri: Wayar wa mata kai ne mafita – Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta bayyana cewa wayar wa da ýaýa mata kai linzami ne na kawar da matsalolin da mata kan yi fama da su a sanadiyar auren wuri.

A cewarta wadannan matsaloli sun hada da rashin samun ingantaccen ilimi na zamani, yoyon fitsari, talauci da sauran su.

Mai Magana da yawun Aisha, Suleiman Haruna ne ya sanar da haka yayin da kungiyar matan dake aiki da gwamnatocin na yankin kasashen Afrika suka ziyarce ta a fadar shugaban kasa a ranar Laraba, 7 ga watan Nuwamba a Abuja.

Auren wuri: Wayar wa mata kai ne mafita – Aisha Buhari
Auren wuri: Wayar wa mata kai ne mafita – Aisha Buhari
Asali: Depositphotos

A Karshe Aisha ta yi kira ga kungiyar da su tsara hanyoyin wayar da kan mata game da mahimmancin samun ilimin Boko tare da yin la’akari da banbancin al’adun bangarorin kasashen Afrika.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta sha kan yan Boko Haram a Yobe, sun dawo da kwanciyar hankali

Sannan kungiyar ta tsaro hanyoyin kawar da matsalolin yin auren wuri da mata da dama ke fama da su domin inganta su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel