Wani ma'aikaci a Kaduna ya rasa aikin sa saboda kaunar Shugaba Buhari

Wani ma'aikaci a Kaduna ya rasa aikin sa saboda kaunar Shugaba Buhari

Wani ma'aikaci da gidan yada labarai na Rediyo da Talabijin a jihar Kaduna na DITV-Alheri mallakar tsohon na hannun damar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rasa aikin sa sakamakon nuna soyayyar shugaba Buhari karara a dandalin sadarwar zamani.

Majiyar mu ta Daily Nigerian ta ruwaito mana cewa shi mai kafar sadarwar zamanin, Mista Baba-Ahmed tsohon na hannun damar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne da yayi masa dan sa ido a zaben shekarar 2019 a jam'iyyar APC kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa PDP.

Wani ma'aikaci a Kaduna ya rasa aikin sa saboda kaunar Shugaba Buhari

Wani ma'aikaci a Kaduna ya rasa aikin sa saboda kaunar Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa shi ma'aikacin da ya rasa aikin sa mai suna Umar Ridwan, ya zargi cewa saboda ya yada wani rubutu ne a shafin sa na dandalin sadarwar zamani dake da alaka da nuna soyayya ga shugaban.

Sai dai kuma mahukun ta a gidan yada labaran sun musanta zargin nasa inda kuma suka ce sun yi niyyar yanke alaka da shi ne kawai sakamakon damar da kundin tsarin mulki ya tanadar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel