Ruwan da aka tafka a daminar bana ya yi mummunar barna a matatar man Dangote

Ruwan da aka tafka a daminar bana ya yi mummunar barna a matatar man Dangote

- Aliko Dangote, ya ce ruwan da aka tafka a daminar bana ya janyo masa babbar asara a aikin da ya ke yi na gina matatar mai, mallakinsa

- Dangote ya ce a watan Ogosta, ya samu damar shirya sama da $4.5bn (a kan bashi) don daukar nauyin ayyukan matatar man

- Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Dangote na cewa masu saka jari, za su zuba akalla $3.15bn, inda babban bankim duniya zai samar da rancen $150m

Shugaban kamfanin masana'antar Dangote Ltd, Aliko Dangote, ya ce ruwan da aka tafka a daminar bana ya janyo masa babbar asara a aikin da ya ke yi na gina matatar mai, mallakinsa. Dangote ya ce, idan har aka kammala ginin, za a rinka tace ganga 650,000 ta mai a kowacce rana, inda za ta dawo aiki gaba daya bayan watanni 6 na shekarar 2020.

A wata hira da yayi da gidan talabijin na Bloomberg, ya ce: "Zamu kamalla dukkanin ayyukan hada injina a karshen 2029, mun fuskanci lalacewar kayayyaki sakamakon ruwan da aka tafka a daminar bana. Duk da hakan, mun farfado yanzu, muna kan kokarin gyara.

"Babbar matatar maice, ita ce ta farko a duniya mai rajin kanta. Zamu fara tace mai a cikin watanni hudu na shekarar 2020. Za mu yi kokarin dai-daita komai, matatar na bukatar fasaha sosai."

KARANTA WANNAN: Wasan taka leda: An dawo cigaba da buga gasar cin kofin zakarun Turai

Ruwan da aka tafka a daminar bana ya yi mummunar barna matatar man Dangote
Ruwan da aka tafka a daminar bana ya yi mummunar barna matatar man Dangote
Asali: UGC

Dangote ya ce a watan Ogosta, ya samu damar shirya sama da $4.5bn (a kan bashi) don daukar nauyin ayyukan matatar man.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Dangote na cewa masu saka jari, za su zuba akalla $3.15bn, inda babban bankim duniya zai samar da rancen $150m, yayin da shi zai sanya jarin kashi 60 daga kudaden sa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel