Gwamnatin Kano ta bada kwangilar N159m don gina wata babbar cibiya a asibitin AKTH

Gwamnatin Kano ta bada kwangilar N159m don gina wata babbar cibiya a asibitin AKTH

- Gwamnatin jihar Kano, ta amince da sakin N159m don bayar da kwangilar gina wata babbar cibiya ta zamani, a cikin asibitin koyarwa na Aminu Kano, (AKTH), da ke a cikin Kano

- Sanarwar ta ce, idan har aka kammala gini, cibiyar za ta kunshi dakin tarbar baki, dakin taro na daraktoci, dakin gwaje gwajen cutuka da magunguna, ofisoshi 7 na ma'aikata

- Sanarwar ta kuma ce cibiyar za ta kuma samu azuzuwa na makarantun gwamnati da za a rinka koyar da kiwon lafiya, dauke da ofisoshi sama da 30

Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da sakin N159m don bayar da kwangilar gina wata babbar cibiya ta zamani, a cikin asibitin koyarwa na Aminu Kano, (AKTH), da ke a cikin Kano.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakiyar daraktan hulda da jama'a na asibitin, Hajiya Hauwa Abdullahi, wacce aka samawa manema labarai a ranar Laraba a Kano.

Sanarwa ta ce, kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Kabiru Getso ne ya sanar da hakan a lokacin da ya ke zagayawa da dan kwangilar da zai aiwatar da ginin a harabar da za a kaddamar da ginin a ranar Talata.

KARANTA WANNAN: Ku warware matsalar da ke tsakaninku da ASUU - Majalisar dattiaji ga gwamnatin tarayya

Gwamnatin Kano ta bada kwangilar N159m don gina wata babbar cibiya a asibitin AKTH
Gwamnatin Kano ta bada kwangilar N159m don gina wata babbar cibiya a asibitin AKTH
Asali: Depositphotos

Sanarwar ta ruwaito Kwamishinan yana cewa gwamnati ta yanke shawarar gina katafaren dakin sayar da magungunan ne, sakamakon wani taron kasa da kasa da aka gudanar kan illolin manyan karafa a cikin ruwa, wanda ya gudana a otel din Tahir Guest Palace a shekarar 2017.

"A wannan taron ne, gwamna Abdullahi Ganduje ya sha alwashin gina wannan katafaren dakin sayar da magungunan don zama babbar cibiyar binciken kiwon lafiya da kuma horas da jami'an kiwon lafiya," a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ce, idan har aka kammala gini, cibiyar za ta kunshi babban dakin tarbar baki, babban dakin taro na daraktoci, babban dakin gwaje gwajen cutuka da magunguna, manyan ofisoshi 7 na ma'aikata, dakin dafa abinci da kuma manyan makewayi.

Sanarwar ta kuma ce cibiyar za ta kuma samu azuzuwa na makarantun gwamnati da za a rinka koyar da kiwon lafiya, dauke da ofisoshi sama da 30.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel