Garau takardun makaranta na suke babu na bogi a cikin su – Isah Ashiru

Garau takardun makaranta na suke babu na bogi a cikin su – Isah Ashiru

Dan takarar kujeran gwamna a karkashin lemar jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, Isah Ashiru ya yi watsi da jita-jita da ke yawo kan cewa wai takardunsa na makaranta duk na bogi ne.

Ashiru a takarda da ofishin yada labaran sa ta fitar, ya ce babu gaskiya cikin zargin jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ashiru ya bukaci magoya bayan sa da su yi watsi da wannan zargi cewa jam’iyyar APC ce ke shirya masa wannan tuggu don ta bata shi a idanun mutanen jihar Kaduna.

“Ina za a ce wai takardun makarantana na bogei ne bayan sau hudu ina takara a kasar nan kuma da su wadannan takardu nayi wadannan takara.”

Garau takardun makaranta na suke babu na bogi a cikin su – Isah Ashiru

Garau takardun makaranta na suke babu na bogi a cikin su – Isah Ashiru
Source: UGC

Ashiru ya ce irin wannan bita da kullin da ake masa ba zai sa ya yi faduwar gaba ba yana mai cewa yana nan daram kuma ya fito da karfin sa don kada jam’iyyar APC a zabe mai zuwa a jihar.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kwamitin shugaban kasa akan yaki da rashawa, Farfesa Itse Sagay (SAAN) ya ce majalisar dokokin jihar Kano ba ta da kayan aikin binciken Gwamna Abdullahi Ganduje wanda ake zargi da karban cin hanci daga dan kwangila.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram na kaddamar da hari a Yobe

Wani bidiyo ya yi fice a yanar gizo inda aka nuna Ganduje yana karban daloli daga hannun dan kwangila, lamarin da ya sa majalisar dokokin jihar kafa kwamitin bincike wanda suka gayyaci gwamnan.

Sai dai wata babbar kotun Jihar Kano ta umurci majalisar dokokin jihar da ta dakatar da binciken a ranar Litinin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel