Antoni Janar: Dalilinmu na rabawa talakawa $322.5m da Abacha ya boye tun a zamaninsa

Antoni Janar: Dalilinmu na rabawa talakawa $322.5m da Abacha ya boye tun a zamaninsa

- Mr Abubakar Malami, ya ce an rabawa talakawa $322.5m da aka gano Abacha boyesu, saboda ganin cewa, sune suke shiga mawuyanci hali sakamakon cin hanci da rashawa

- Ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin, a wani taron tattaunawa da kungiyoyin fararen hula da ke fafutukar ganin an samar da doka ta musamman kan laifukan ta'addanci

- Malami ya ce Buhari ya bashi umurnin gano kadarorin gwamnati da aka sace da kuma alkintasu ta yadda za a yi amfani da su wajen bunkasa rayuwar al'ummar kasar

Antoni Janar, kuma ministan shari'a, Mr Abubakar Malami, ya ce gwamnatin tarayya ta yanke shawarar rabawa talakawan Nigeria $322.5m da aka gano Abacha ya handame tare da boyesu tun a zamanin mulkinsa, don tabbatar da cewa, wadanda ke shiga mawuyanci hali sakamakon cin hanci da rashawa ne suka amfani da kudaden.

Ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin, a wani taron tattaunawa da kungiyoyin fararen hula da ke fafutukar ganin an samar da doka ta musamman kan laifukan ta'addanci, taron da ya gudana a Abuja.

Ya ce bin diddigi da gano kudaden da wasu shuwagabanni ko 'yan siyasa, koma dai suwaye suka sata na jama'a suka boye, na daga cikin yunkurin kawo karshen cin hanci da gwamnati mai ci a yanzu ta sanya gaba, yana mai cewa babban abun da ake so shine tabbatar da cewa anyi amfani da kudaden da aka gano ta nhanyar da zata shafi rayuwar 'yan Nigeria kai tsaye musamman ma talakawa daga cikinsu.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Kungiyar kwadago ta janye shiga yajin aiki, gwamnati za ta biya N30,000

Antoni Janar: Dalilinmu na rabawa talakawa $322.5m da Abacha ya boye tun a zamaninsa
Antoni Janar: Dalilinmu na rabawa talakawa $322.5m da Abacha ya boye tun a zamaninsa
Asali: Twitter

"A wannan yunkurin ne, gwamnati, tare da hadin guiwar abokan huldarta na kasashen waje, suka amince da amfani da dala miliyan 332.5 da aka gano a kasar Switzerland, wajen gudanar da shirin tallafawa 'yan Nigeria marasa karfi da N5,000 a kowanne wata," a cewar sa.

Antoni Janar, wanda Mrs Ladidi Mohammed, darakta a sashen gano kadarorin gwamnati da alkinta su, ta karanta jawabin nasa, ya ce yajin dadin yadda kungiyoyin fararen hular suka cusa kawunansu a cikin sha'anin bin diddigi kan yadda rabon ya kasance.

Malami ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi umurnin daukar dukkanin matakan da suka dace na ganin cewa an gano kadarorin gwamnati da aka sace da kuma alkintasu ta yadda za a yi amfani da su wajen bunkasa rayuwar al'ummar kasar.

Ya yi amfani da wannan taron, wajen yin kira ga majalisun tarayya da su tabbata sun amince da wannan sabon kudurin doka kan aikata laifukan ta'addanci kafin karshen shekarar 2018.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel