PenCom ta bankado yadda 'yan damfara ke karbar hakkokin matattu alhalin suna raye
- Wasu yan damfara, sun fara fakewa da sunan 'yan uwan wasu ma'aikata da suka yi ritaya, don karbar hakkokin tsoffin ma'aikatan da sunan sun mutu
- Hukumar PenCom ta bayyana cewa tana kokarin daukar matakai da zasu dakile aika aikar yan damfarar
- PenCom ta ce daga cikin matakan da za ta dauka akwai bullo da sabon tsari, da zai karfafa asusun PFAs wajen tafiyar da harkokinsu
Wasu yan damfara da ba a bayyana ko suwaye ba, sun fara gudanar da aika aikarsu ta hanyar fakewa da sunan 'yan uwan wasu ma'aikata da suka yi ritaya, karkashin shirin baiwa tsoffin ma'aikata hakkokinsu, inda suke zuwa wajen jami'an asusun shirin don karbar kudi a madadin tsoffin ma'aikatan.
A cewar bayanan da aka samu daga hukumar fansho ta kasa, yan damfarar, wadanda ke amfani da takardun bogi, na kaiwa jami'an asusun na PFAs, a matsayin takardun tsoffin ma'aikatan, inda har suka samu nasarar karbar hakkokin wasu tsoffin ma'aikatan da takardun shaidar cewa matattu ne.
Hukumar PenCom ta bayyana cewa tana kokarin daukar matakai da zasu dakile aika aikar yan damfarar.
KARANTA WANNAN: Yanzu Yanzu: Buhari ya sake ganawa da Tinubu

Asali: Twitter
Hukumar ta bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ta bayar mai dauke da taken 'Sabunta hanyoyin karbar hakkokin ma'aikatan da suka mutu', wacce kuma ta aikewa asusun na PFAs.
A cewar wannan sanarwa, "hukumar ta samu korafe korafe daga wadanda suka yi ritaya, wadanda suka yi zargin cewa Asusun PFAs ya biya cikakkun hakkokinsu ga magadansu ko wasu wakilansu, duk da cewa suna a raye kuma ba tare da saninsu ba.
"Biyo bayan wadannan korafe korafe da kuma rahoto daga PFAs, ya zama wajibi a sake daukar wasu kwararan matakai da zasu kawo karshen korafe korafen da kuma inganta tsarin karbar kudaden wadanta suka yi ritaya walau suna raye ko sun mutu."
PenCom ta ce daga cikin matakan da za ta dauka akwai bullo da sabon tsari, da zai karfafa asusun PFAs wajen tafiyar da harkokinsu da kuma kara zurfafa bincike kan takardun da magada ko wakilan wasanda suka yi ritayar suka gabatar kafim amincewa da biyan kudaden.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Wannan zai kyautata alakarmu da kai mai bibiyarmu. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don ci gaba da karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng