El-Rufai ya zabi mace a matsayin abokiyar takara
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya sanar da zabar Hadiza Balarabe a matsayin abokiyar takararsa a zaben 2019.
A wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa, Samuel Aruwan, gwamnan ya ce da gan-gan aka zabi Misis Hadiza domin karfafa wa mata gwiwar shiga gwamnati.
Mataimakin gwamna mai ci, Barnabas Bala, ya koma neman kujerar majalisar dokokin kasar kuma tuni ya zamo dan takarar APC a yankin kudancin Kaduna.

Source: Depositphotos
“Akwai kwamishinoni mata biyar a majalisarsa ta mutane 14, wanda hakan bah aka yake ba gwamnonin da suka fi shi yawan yan majalisa. A tarihin Kaduna wannan ne karo na farko da wata babbar jam’iyyar siyasa ta zabi mace a matsayin abokiyar takara,” cewar sanarwan.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: WAEC ta gabatar da takardan shaida ga Shugaba Buhari
Misis Hadiza ce babbar sakatariyar hukumar lafiya ta jihar Kaduna a yanzu, matsayin da take rike da shi tun a watan Fabarairun 2016.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng