Amurka ta yi martani kan rikicin sojoji da ’yan Shi’a
Gwamnatin kasar Amurka ta nuna alhini akan rikicin da ya afku a tsakanin mabiya kungiyar Shi’a masu zanga-zanga da kuma sojojin Najeriya babbar birnin tarayya Abuja da kuma kewaye.
Rahotanni sun nuna cewa kashe mabiya kungiyar ta Shi’a da dama, a tsakanin ranakun Asabar zuwa ranar Talata, bayan da sojojin suka zarge su da jifar su da dutse da sauran wasu makaman hannu da harbi da gwafa.
Cikin wani jawabi da Ofishin Jakadanci Amurka a Najeriya ya buga a shafin sa na internet, Amurka na yin kiran da a gudanar da bincike mai tsanani da kuma gano musabbabin barkewar rikicin.

Asali: Original
“Mu na kira da hukumomin Gwamnatin Najeriya da a gaggauta gudanar da bincike tare da daukar tsatstsauran mataki kan wadanda ke da laifi karya dokar Najeriya. Sannan kuma mu na kiran bangarorin biyu kowa ta daina.”
KU KARANTA KUMA: Bidiyon cin hanci: Ganduje ya tura wakili zuwa majalisar dokokin jihar Kano
Kimanin mabiya Shi’a 491 aka kama, kuma a ranar Alhamis aka gurfanar da 120 daga cikin su a kotu, a Abuja.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng