Taka leda: Neymar na iya fuskantar hukuncin zaman wakafi saboda komawarsa Barcelona

Taka leda: Neymar na iya fuskantar hukuncin zaman wakafi saboda komawarsa Barcelona

- Wata kotun majistire da ke kasar Sifaniya ta ce akwai yiyuwar dan wasan taka ledan na kasar Brazil na iya fuskantar zaman wakafi na tsawon shekaru shida

- A watan Mayun 2013 ne Neymar ya koma Barcelona akan kudi Euro miliyan 57.1, sai dai kungiyar DIS ta ce akwai rufa rufa kan gaskiyar kudin da aka kashe na komawarsa

- Saboda kasancewar wa'adin shekarun zaman wakafin ya zarce shekaru 5, ana sa ran alkalai 3 ne za su gudanar da shari'ar, wacce ake tsammanin za a gudanar da ita a Audiencia Nacional

Wata kotun majistire da ke kasar Spain da ke gudanar da bincike kan wani zargi da ake yi na saba ka'idoji da ke tattare da komawar Neymar zuwa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a 2013, ta ce akwai yiyuwar dan wasan taka ledan na kasar Brazil na iya fuskantar zaman wakafi na tsawon shekaru shida.

"Hukuncin laifin nasa na iya sawa ya yi zaman wakafi na shekaru 4, ko shida," a cewar wata sanarwa da mai shari'a Jose Maria na kotun ua bayar a yau Laraba.

Neymar, iyayensa, shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Jesep Bartomeu da kuma mai kula da shi Sandro Rosell na zaman jiran fara shiga kotun tuhuma kan zargin cin hancin da aka tafka a komawar Neymar babbar kungiyar kwallon kafa a wasan La Liga na 2013.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: EFCC ta bankado yadda tsohon gwamnan Filato ya karkatar da N6.3bn

Taka leda: Neymar na iya fuskantar hukuncin zaman wakafi saboda komawarsa Barcelona
Taka leda: Neymar na iya fuskantar hukuncin zaman wakafi saboda komawarsa Barcelona
Asali: Getty Images

Shari'ar, wacce ta biyo bayan wani korafi da kungiyar DIS, wacce ke da wani alhakin kaso akan rayuwar Neymar, ta shigar, na kunshe da batu kan cin hanci da ashawa da kuma damfara, a tattare da komawar dan wasan zuwa Barcelona.

A watan Mayun 2013 ne Neymar ya koma Barcelona akan kudi Euro miliyan 57.1. Duk da cewar babu wani bayani a takarda daga kungiyar kwallon kafa ta Brazil da ke Santos, dangane da kudaden da aka kayyade kan sauyin kungiyar kwallon kafar, sai dai ana zargin iyayen Neymar sun karbi Euro 40m, yayin da FC Santos ta karbi Euro 17.1m.

A watan Janairu 2014, masu shigar da kara a Madrid suka fara gudanar da bincike kan wannan canjin kungiyar kwallon kafa sakamakom takardar da hukuma ta bukata na kunshe da wasu bayanai masu rikitarwa.

Rosell ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban Barcelona mako daya da faruwar hakan, ita kuma Barcelona ta bayyana cewa ta biya Euro 86.2m akan sayo dan wasan na kasar Brazil.

DIS, wacce ta karbi Euro 6m daga Euro 17.1m da FC Santos ta karba, ta yi zargin cewa Barcelona sa FC Santos sun yi rufa rufa akan ainihin kudin da aka kashe kan dan wasan na komawarsa Barcelona.

A yanzu, ana sa ran Bartomeu, Rosell, Barcelona, FC Santos da kuma tsohon shugaban kungiyar, Odilio Rodrigues Filho, za su amsa tuhumar da ake masu ta yin almundahana da damfara, a cewar takardar kotun.

Saboda kasancewar wa'adin shekarun zaman wakafin ya zarce shekaru 5, ana sa ran alkalai 3 ne za su gudanar da shari'ar, wacce ake tsammanin za a gudanar da ita a Audiencia Nacional, wata babbar kudin lardi da ke Spaniya, da kuma batu kan karya dokar kasa da ke karkashin kotun lardin kasar.

Sai dai, babu wanda zai iya hasashen ko Neymar zai yi zaman wakafin ko kuma zai tsallake rijiya ta baya baya.

SANARWA: A kwanan nan ne shafin jaridar NAIJ.com ya sauya suna zuwa Legit.ng Wannan kuwa babban sauyi ne da zai kyautata alakarmu da kai mai bibiyarmu. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da shafinmu na Legit.ng don ci gaba da karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel