Sokoto 2019: Yadda rikicin Tambuwal, Bafarawa da Wamakko zai kasance

Sokoto 2019: Yadda rikicin Tambuwal, Bafarawa da Wamakko zai kasance

Kai tsaye ka yi hasashen yadda rikicin siyasar da ya mamaye jihar Sokoto zai iya kasancewa a 2019 zai zama abu mai matukar wahala, musamman tsakanin jam'iyyar PDP mai mulki a jihar da kuma APC mai mulki a kasar.

Fafutukar samun lashe zaben kujerar gwamnan jihar a zabe mai zuwa wani babban al'mari ne da har yanzu yake kasa yana dabo, ga shi kansa gwamnati mai ci, Aminu Waziri Tambuwa, mataimakinsa, Ahmed Aliyu Sokoto. Kasancewar gaba dayansu sun ci gajiyar Sanata Aliyu Magatakarda Wammako ne idan har aka zo fagen uban gida na siyasa, da rawarsa ne har suka samu nasarar zaben 2015.

Sai dai a yanzu rikiin ya dauki sabon salo, tun bayan sauyin shekarar Tambuwal daga APC zuwa PDP da kuma zaman Wamakko a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar. Wannan ya tabbatar da cewa babu sauran wata alaka mai karfi a tsakaninsu, duk da an san cewa akwai kyakkyawar dangantaka mai karfi a tsakaninsu.

KARANTA WANNAN: Kiwon lafiya: Sabuwar cutar 'Shan Inna' ta bulla Daura da wasu garuruwan jihar Katsina

Sokoto 2019: Yadda rikicin Tambuwal, Bafarawa da Wamakko zai kasance
Sokoto 2019: Yadda rikicin Tambuwal, Bafarawa da Wamakko zai kasance
Asali: Twitter

A wani taron zantawa da magoya bayansa da ya gudanar a gaban gidan gwamnatin jihar Sokoto, Tambuwal ya gargadi jam'iyyar adawa da kada su bari ransa ya baci. Ya shaida cewa akwai sirruka da dama da ya ke boyewa, wanda idan har aka kaishi bango, to zai fasa kwai, lamarin da ya tabbata ba zai yiwa kowa dadi a 'yan siyasar jihar ba.

A nashi bangaren kuwa, masu fashin baki na ganin wasu kalamai da Wammako ya taba yi na cewar a baya ya san Tambuwal a matsayin dan siyasa mai rike alkawari da kima, amma sauya shekarsa ya goge dukkanin wadannan martabobi, hakan kamar Wamakko na san jan layi tsakaninsa da Tambuwal musamman a fuskantar aben 2019.

KARANTA WANNAN: Kotu ta dage karar da aka shigar ta bukatar majalisun tarayya su tsige Buhari

Sokoto 2019: Tambuwa, Bafarawa
Sokoto 2019: Tambuwa, Bafarawa
Asali: UGC

Kamar dai yadda Wamakko ya zabi Tambuwal a matsayin wanda zai gaje shi bayan kammala wa'adinsa a 2014, a wannan karon ma, ana sa ran cewa Wamakko zai sake neman wanda zai kara da gwamnan jihar na yanzu, ta hanyar hadin guiwa da sauran kusosin siyasar jihar don tabbatar da cewa ya tunkude Tambuwal daga mulki.

A yanzu dai, kowa ya san inda aka dosa, tun bayan sauya shekar Tambuwal zuwa PDP da kuma sake yin hadin guiwa da tsohon gwamnan jihar Attahiru Dalhatu Bafarawa da sauran jiga jigan 'yan siyasa a jihar, hakan ya tabbatar da cewa zaben 2019 a jihar Sokoto zai karkata ne kan 'wanda ya fi karfi ya kwata'.

KARANTA WANNAN: Karin bayani: Yadda ganawar Buhari da gwamnonin Kudu maso Kudu ta kasance

Idan har ba a manta ba, a 1999, Bafarawa da Wamakko, gwamna ne da mataimakinsa, sai dai sun raba gari bayan kammala wa'adin mulkinsu karo na biyu, tun bayan da shi Bafarawa ya nuna sha'awar tafiya da Alhaji Ibrahim Maigari Dingyadi a matsayin mataimakinsa, wanda hakan ba shi ne tsarin Wamakko ba.

Duba da tarihi na maimaita kansa, jihar Sokoto dai na daya daga cikin jihohin da gwamna mai ci baya goyon bayan mataimakinsa ya gaje shi, Wamakko ne dai ya kawo Tambuwal a matsayin mataimakinsa. Yanzu kuma da Tambuwal, ya fice daga APC zuwa PDP, shi kuma Wamakko ya nada mataimakin sa a matsayin dan takarar gwamnan jihar karkashin APC, abun tambayar a nan shine, shin Tambuwal zai kara da mataimakinsa ne ko uban gidansa?

Duk da cewa, wasu jiga jigai a jihar kamar su Bafarawa, Umarun Kwabo da kuma 'yan majalisun dokoki 19 cikin 30 na majalisar dokokin jihar, shuwagabannin kananan hukumomi 23 da kuma kwamishinonin jihar za su goyi bayan Tambuwal, sai dai har wane mataki zai kai wajen rushe sunan 'Sai Alu' da kullum ke yawa a jihar Sokoto?

Lallai, neman samun nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jihar Sokoto zai zo da sabon salo kuma sabon rikici a 2019.

SANARWA: A kwanan nan ne shafin jaridar NAIJ.com ya sauya suna zuwa Legit.ng Wannan kuwa babban sauyi ne da zai kyautata alakarmu da kai mai bibiyarmu. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da shafinmu na Legit.ng don ci gaba da karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel