Hukumar Hizbah ta cafke kasurgumin kwarto da ke zina da matan aure a Kano
Hukumar Hizbah dake da alhakin tabbatar da da'a a tsakanin al'umma ta jihar Kano dake a Arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke wani kasurgumin kwarto da ya shahara wajen yin lalata da matan aure.
Daya daga cikin kwamandojin Hizbah din kuma mai magana da yawun ta, Ustaz Salisu rijiyar Lemo shine ya sanar wa da al'umma hakan a cikin wani dogon rubutu da yayi a shafin hukumar na dandalin sadarwar zamani.
Legit.ng Hausa ta samu cewa kasurgumin kwarton, wanda aka sakaya sunan sa kamar yadda hukumar ta Hizbah ta labarata, yana ikirarin bayar da maganin aljannu ne ga matan auren inda daga nan ne kuma yake anfani da wannan damar wajen labbatar su.
Dubun sa ta cika ne dai a lokacin da ya labbaci wata kanwar abokin sa wacce ita ma matar aure ce da ya kira a wani otel ya kuma yi zina da ita bayan ya bata maganin aljannun kafin hukumar ta damke shi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng