Minti 2 kawai miji na keyi, ku raba mu - Wata mata 'yar Arewa ta roki kotu

Minti 2 kawai miji na keyi, ku raba mu - Wata mata 'yar Arewa ta roki kotu

Wata matar aure mai suna Hauwa Adamu a ranar Larabar da ta gabata ta roki kotun jiha a unguwar Mararaba, jihar Nasarawa da ta taimaka ta raba auren su da mijin ta domin baya gamsar da ita a rayuwar su ta aure.

Hauwa ta shaidawa kotun dai cewa ita ta gaji da auren na su domin mijin ta iyakar sa mintuna biyu kacal idan suka zo kwanciyar Aure, abun da ta bayyana da cewa yayi mata kadan matuka, zargin da mijin shi kuma ya karyata.

Minti 2 kawai miji na keyi, ku raba mu - Wata mata 'yar Arewa ta roki kotu
Minti 2 kawai miji na keyi, ku raba mu - Wata mata 'yar Arewa ta roki kotu
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Yan Luwadi da madigo sun fadi wanda za su zaba a 2019

Legit.ng Hausa ta samu cewa haka zalika Hauwa ta kara da cewa tun lokacin da suka yi aure har yanzu ba ta taba samun ciki ba, lamarin da yake damun ta matuka domin tana son 'ya'ya kuma abun takaici shine yadda mijin na ta ke zargin ta da zubda cikin da dama bata taba samu ba.

Matar dai ta shaidawa kotun cewa ita a shirye take da ta biya mijin kudin sadakin sa da ya bata duk domin ya sauwake mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng