Mafusatan 'yan gari sun fatattaki wani basaraken gargajiya daga fadar sa a Najeriya
Da akwai alamun tashin-tashina a garin Ilogbo dake a karamar hukumar Ido/Osi dake a jihar Ekiti ta kudu maso gabashin Najeriya yayin da mafusatan 'yan gari suka fatattaki Sarkin garin daga masarautar sa.
Kamar dai yadda muka samu, mafusatan 'yan garin dai sun zargi daya daga cikin 'ya'yan basaraken ne mai suna Adeleye da jagorantar wasu 'yan daba da suka yi sanadiyyar ajalin wani matashi mai suna Bolu.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Mutumin da ya hau dogon karfe sai Atiku ya zo ya shiga hannun 'yan sanda
Legit.ng Hausa ta samu cewa'yan garin dai sun yi zargin cewa basaraken ya kasa yin katabus ne a wajen tarbiyyar 'ya'yan sa kuma har ya zuwa bayan aukuwar lamarin bai ce uffan ba, wanda hakan ne ya tunzura su.
Sai dai kuma jami'an 'yan sanda jihar a ta bakin jami'in hulda da jama'ar su Mista Caleb Ikechukwu ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da bada tabbacin fara kama wasu daga cikin masu laifin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng