Karshen Alewa: An cafke tsohon ma'aikacin banki da ya sace N8.7m ta kafar yanar gizo
- Ana tuhumar Kazeem Alli da aikata laifuka 3, da suka hada zamba, yin kutse ga bayanan wani da kuma satar N8.7m ta kafar yanar gizo
- Sai dai wanda ake zargin, ya ce sam bai aikata wannan laifi da ake zarginsa da aikatawa ba
- Mai shari'a Obiozor ta bayar da umurnin tsare mai laifin a gidan kaso har sai zuwa lokacin da za aci gaba da sauraron karar da duba yiyuwar bada belinsa
A ranar Litinin ne aka gurfanar da wani tsohon ma'aikacin bankin 'Union Bank Nigeria Plc', Kazeem Alli, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke da zama a Legas, bisa zarginsa da almundahanar kudi har N8.7m ta hanyar kafar yanar gizo.
Alli wanda hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa da kuma yiwa dukiyar al'umma zagon kasa EFCC, ta gurfanar da shi, ana tuhumarsa da aikata laifuka 3, da suka hada zamba, yin kutse ga bayanan wani da kuma satar N8.7m ta kafar yanar gizo.
Wanda ake zargin, da ba a bayyana inda yake da zama ba, ya gurfana ne gaban mai shari'a (Farfesa) Chuka Obiozor.
KARANTA WANNAN: PDP ta zargi fadar shugaban kasa da kare korarren shugaban hukumar NHIS
EFCC ta ce wanda ake zargin ya hada kai da wasu mutane da dama, wajen yin kutse ga bayanan wani kwastoman bankin na 'Union plc', mai suna Alexander Cherembem, don kwashe kudin da ke cikin asusun mutumin ta yanar gzio.

Asali: Twitter
Haka zalika hukumar ta zargi tsohon ma'aikacin bamkin, cewar a 8 ga watan Mayu, 2018, a lokacin yana ma'aikacin bankin na 'Union Bank of Nigeria Plc, ya gaza samun bayanan sirrin kwastoman bankin, ta asusunsa mai lamba 0010807900.
Ana zarginsa da yi kutse a asusun Alexander Cherembem Okan, tare da kwashe N8.677,907.00m daga asusun mai lamba 0010807900.
A cewar EFCC, wanda ake zargin, ya aikata laifin da ya cancanci hukunci a sashe na 22, 22(2) da kuma sashe na 37 na laifukan yanar gizo, a dokar 2015.
Sai dai wanda ake zargin, ya ce sam bai aikata wannan laifi da ake zarginsa da aikatawa ba.
KARANTA WANNAN: Oshiomhole ya yi watsi da rahoton da ke cewa gwamnonin APC na kitsa tuggun tsige shi
A kan wannan kin amincewar tasa, lauya mai kare wanda ake zargin, ya bayyanawa kotu kudirinsa na bukatar belin wanda yake karewa tare da bukatar kotun da ta dage sauraron karar don bashi lokacin gabatar da hujjoji.
Lauyan masu karar, Chia-yakua bata kalubalanci wannan bukata ta lauya mai kare wanda ake karar ba. Haka zalika, mai shari'a Obizoro ta dage sauraron karar har sai 5 ga watan Nuwamba, wanda a nan ne kuma za a duba yiyuwar bada belin wanda ake zargin.
Mai shari'a Obiozor ta bayar da umurnin tsare mai laifin a gidan kaso har sai zuwa lokacin da aka dawo don ci gaba da sauraron karar da duba yiyuwar bada belinsa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng