Kwastam sun kama kwantena cike da jar miya wanda ya kai N27m daga China

Kwastam sun kama kwantena cike da jar miya wanda ya kai N27m daga China

Rahotanni sun kawo cewa hukumar kwastam na Najeriya sun kama kwantena cike da jar miya (dage-dage) da wasu kayayyaki da kudinsu ya kai kimanin N27,960,000 wanda aka shigo da su daga kasar China.

Hukumar Kwastam ta kama Kwantenan wanda aka shigo da ita a tashar jirgin ruwa dake Legas bayan jita-jitan da sashin basirar hukumar ta gabatar.

Yayinda yake yiwa manema labarai jawabi a Legas a ranan Juma’a a lokacin da yake bayyana wasu daga cikin kayayyakin da hukumar ta kace tsakanin 19 ga watan Satumba da 18 ga watan Oktoba, 2018, mataimakin shugaban kuma mai zartarwa na sashin hukumar na kasa CGC, Abdullahi Kirawa yace tsarin yayi tsanani har ya kai ga cewa yan Najeriya suna shigo da miya kasar.

Kwastam sun kama kwantena cike da jar miya wanda ya kai N27m daga China
Kwastam sun kama kwantena cike da jar miya wanda ya kai N27m daga China
Asali: UGC

Yayi korafi cewa tukwanen miyan da swauran kayan abinci da aka shigo dasu suna dauke da rubuce rubucen harshen China, kuma hakan yasa an kasa tantance su, wanda hakan na iya kasancewa babban illa ga wadanda za su ci.

KU KARANTA KUMA: Babu wani hadin kai da Fayose ke ba hukumar EFCC - Hadiminsa

Yace wasu daga cikin kayayyakin ma tuni sun kara yin tsatsa a cikin kwantenan, cewa hakan ya nuna illar su ga lafiyar al’umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel