'Yan a-mutun Buhari 5 da yanzu haka ake tuhuma da tafka satar Naira biliyan 232
Yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin al'amurran da shugaba Muhammadu Buhari yayi kaurin suna wajen su kuma yake yakin neman zaben sa da su tun bayan shigowar sa siyasa a shekarar 2002.
Shi dai shugaban kasar ya samu kyakkyawar shaida game da gaskiyar sa da kuma irin yadda duk da irin binciken sa da aka yi a baya da kuma mukaman da ya rike, ba'a taba samun sa da laifin cin hanci da rashawar ba.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta saki alkaluman kasafin kudin 2019
Sai dai ba a nan gizo ke sakar ba domin kuwa yanzu ana zargin cewa shugaban ya zagaye kan sa ne da manyan barayin da ake zargi da tafka babbar sata ta makudan kudade a kujerun da suke rike a baya.
Hakan dai na jefa shakku matuka a zuciyoyin al'umma wadanda suke ganin hakan tamkar tufka ce da warwara akan batun na yaki da cin hanci da rashawar da yake ikirarin yi.
Nan ma dai ga jerin wasu mutane nan da suke goyon bayan shugaban kasar kuma suna da zarge-zarge na almundahana da dukiyar al'ummar su da ta kai Naira biliyan 232.
1. Abdullahi Adamu (N15bn)
2. Aliyu Wamakko (N15bn
3. Godswill Akpabio (N100bn
4. Orji Uzor Kalu (N3.2bn)
5. Abdul’aziz Yari (N680m)
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng