'Yan Shi'a sun nemi ganin Buhari akan Sheikh Zakzaky (hotuna)

'Yan Shi'a sun nemi ganin Buhari akan Sheikh Zakzaky (hotuna)

Akalla tsawon shekara daya kenan da yan kungiyar Musulman Shia ke suntirin yin gangami a babbar birnin tarayya Abuja duk akan bukatar su na neman gwamnatin tarayya ta saki shugaban su Ibrahim El-Zakzaky wanda ke tsare.

Kimanain shekaru uku kenan da aka tsare shugaban nasu tun a watan Disamban 2015 a garin Zariya bayan arangama da yan kungiyar suka yi da tawagar rundunar sojin Najeriya.

Daga bisani salon nasu ya fara sauyawa inda suka fara rubuce-rubuce a manyan allunan talla da kuma jikin gine-ginen gwamnatin na batanci ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

'Yan Shi'a sun nemi ganin Buhari akan Sheikh Zakzaky (hotuna)
'Yan Shi'a sun nemi ganin Buhari akan Sheikh Zakzaky
Asali: Facebook

Kwanakin baya sun je ma'aikatar Sharia suka rufe suna masu fadin ba a yi musu adalci ba. Ko a makonni biyu da suka gabata, dandazon 'yan Shi'a sun nufi fadar Shugaban kasa wato Villa, inda suka dinga ikirarin sai sun je da karfi, suna masu fadin a sake musu Malaminsu.

'Yan Shi'a sun nemi ganin Buhari akan Sheikh Zakzaky (hotuna)
'Yan Shi'a sun nemi ganin Buhari akan Sheikh Zakzaky
Asali: Facebook

'Yan Shi'a sun nemi ganin Buhari akan Sheikh Zakzaky (hotuna)
'Yan Shi'a sun nemi ganin Buhari akan Sheikh Zakzaky
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fayemi ya halarci taron tattalin arziki na kasa yayinda aka nemi Tambuwal da Ahmed aka rasa

A bangaren jami'an tsaro sun hana su shiga sun nemi da su kawo a rubuce cewa suna so su ga Buhari akan Malaminsu. Inda a yau suka rubuta takardar suka mika ga jami'an tsaro da alkawarin za su mika korafin ga shugaba Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng