Aisha Alhassan: Dalilina na kwashe kujeru, na'urori da saurasu daga ofishin APC na Taraba
- Aisha Alhassan, ta bayyana dalilinta na kwashe na'urori, kujeru, da sauran kayayyakin da ta sanya a ofishin jam'iyyar APC na jihar Taraba
- Mama Taraba ta ce la'akari da irin cin fuskar da APC tayi mata, da kuma sauya shekarta, bai kamata ace jam'iyyar na amfani da kayan da ta saya da kudinta ba
- Sai dai APC a jihar Taraba sun yi Allah-wadai da wannan mataki da 'yar takarar gwamnan jihar karkashin UDP ta dauka
Tsohuwar ministar mata Aisha Alhassan, wacce a baya bayan nan ta yi murabus daga wannan mukamin nata tare da ficewa daga jam'iyyar APC, ta bayyana dalilinta na kwashe na'urori, kujeru, da sauran kayayyakin da ta sanya a ofishin jam'iyyar APC na jihar Taraba, a lokacin da ta ke cikin jam'iyyar.
Mr Aaron Artimas, sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC a jihar Taraba, ya bayyana cewa Aisha Alhassan ta kuma cire na'urori masu busa sanyi, tebura tebura da kuma kafet da ta sayawa jam'iyyar. "Muna Allah wadai da wannan hukunci da ta yanke."
"Tsohuwar minsitar ta kwashe komai data sanya a cikin ofishin a lokacin da take mambar jam'iyyar APC," a cewar Artimas, a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Jalingo.
KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Wani gini mai hawa 3 da ya rushe a Anambra ya rutsa da ma'aikata 11 a ciki

Asali: Twitter
Sai dai da take kare kanta, Aisha Alhassan ta ce ba itace ta bayar da umurnin a cire kayayyakin ba, illa dai ta amince da wannan matakin, musamman ganin irin rashin adalcin da jam'iyyar ta yi gareta.
"Ni na sayo kayan da kudina; a lokacin da mai gidana ya sanar dani cewa zasu je su cire kayayyakin daga sakatariyar jam'iyyar, na amince masu da hakan, kasancewar bai kamata APC ta ci gaba da mallakar wani abu nawa ba," kamar yadda ta shaidawa kamfanin NAN a Abuja. Ta karyata jita jitar cewa an kai kayan Abuja bayan ciro su daga Jalingo.
"Babu yadda za ayi in kawo kayan Abuja. Idan da ace nice na bar jam'iyyar a kashin kaina, to da ba zan damu da kayan ba, amma kowa ya san dalilin da ya sanya na fice, sun kitsa wani tuggun ne kawai na yimin kora da hali," a cewarta.
A baya baya dai NAIJ.com ta ruwaito maku cewa Alhassan, wacce jam'iyyar APC ta hana tikitin takarar gwamnan jihar Taraba, ta yi murabus daga kujerarta ta ministar harkokin mata, haka zalika ta sauya sheka zuwa jam'iyyar UDP inda ta samu tikitin tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar a zabe na 2019.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng