Dalilin zuwa na sulhun Obasanjo da Atiku - Gumi (bidiyo)

Dalilin zuwa na sulhun Obasanjo da Atiku - Gumi (bidiyo)

Babban malamin nan na Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana dalilinsa na zuwa wajen sulhunta tsakanin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

A ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba ne Gumi ya bi tawagar Atiku Abubakar zuwa gidan Obasanjo domin sasanta tsakaninsu.

A cewarsa yayi koyi ne da annabi Muhammad, domin cewa ko a zamaninsa ya halarci sulhu a tsakanin yahudawa don wanzar da zaman lafiya.

Gumi yace shugabannin biyu ne suka bukaci a gayyaci wanda babu ruwan shi da bangaranci, don haka aka zabo shi saboda shi babu ruwan shi da wani.

Dalilin zuwa na sulhun Obasanjo da Atiku - Gumi (bidiyo)
Dalilin zuwa na sulhun Obasanjo da Atiku - Gumi (bidiyo)
Asali: Facebook

Cewa duk wanda yake ganin bai yi daidai ba akan haka toh babu shakka shi bamaguje ne domin bai son zaman lafiya.

KU KARANTA KUMA: Ina fuskantar matsin lamba kan barin APC - Yari

Ya ce ya zama dole ya je domin ganin an wanzar da zaman lafiya a fadin kasar. Ya jadadda cewa shi bai ce a zabi wani ba kawai sulhu ya je.

Malamin ya kara da cewa ko gobe aka kira shi yin sulhu zai je.

Ya jadadda cewa masu fadin cewa an bashi dala, kage ne cewa babu wanda ya bashi kudi shi saboda Allah yayi.

Ga cikakken biyon bayanin nasa a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel