Yan Nigeria 10,000 ne suka dawo Nigeria daga kasar Libya - NEMA
- NEMA ta ce sama da 'yan Nigeria 10,000 ne suka yanke shawara tare da dawowa gida a kashin kansu daga kasar Libya
- Hukumar ta ce sun sauka kasar nan a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas da misalin karfe 3:10 na safe
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce sama da 'yan Nigeria 10,000 ne suka yanke shawara tare da dawowa gida a kashin kansu daga kasar Libya, kama daga watan Afrelun 2017 zuwa watan Oktobar 2018.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa Kodinetan hukumar NEMA a shiyyar Kudu maso Yamma, Mr. Yakubu Suleiman ne ya bayyana hakan a lokacin da ya marabci wasu 'yan Nigeria 161 da suka dawo kasar, a filin jirgin sama na Legas.
Suleiman ya ce an tallafawa wadanda suka yanke shawarar dawowa, ta hanyar daukosu ne a rukunai 50, da taimakon hukumar kula da shige da fice ta kasa da kasa IOM.
KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta cafke mutane 2 da suka yiwa 'yar wata 9 fyade
A cewarsa, sun sauka kasar nan a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas da misalin karfe 3:10 na safe, kuma sun samu tarba daga jami'an NEMA da sauran hukumomi a filin jirgin.
Ya ce 147 daga cikin 161 da suka dawo manyan mutanene, yayin da 4 kananan yara ne, sai kuma jarirai 10, yana mai karawa da fadin 12 daga cikin matan na dauke da juna biyu, a bangare daya kuwa 9 daga cikinsu na bukatar kulawar likita.
Suleiman ya yi nuni da cewa a 9 ga watan Oktoba, NEMA ta karbi wasu mutane 149, wanda hakan ya sa suka tashi jimillar 310 a cikin wannan makon.
Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng