Anyi jana’izar shugaban NRC, Usman Abubakar a Abuja
Anyi jana’izar Shugaban hukumar jiragen kasa na Najeriya, Injiniya Usman Abubakar wanda ya rasu a babban birnin tarayya Abuja a yau Juma’a, 12 ga watan Oktoba.
Usman ya rasu a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba yana da shekaru 68 a duniya.
Marigayin ya fito daga karamar hukumar Sandamu dake jihar Katsina.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada shi a matsayin shugaban hukumar NRC a ranar 27 ga watan Satumba 2016. Yayi aiki a matsayin kwamishinan ayyuka a jihar Katsina a shekarar 1987.
KU KARANTA KUMA: Zan ci gaba da shugabancin Obasanjo ne idan nayi nasara - Atiku
Lokuta daban-daban yayi shugabancin Jebba Paper Mills, Daura Tannery, da kuma Interlinked Technologies, kamfanoni masu zaman kansu.
Ya rasu ya bar mata daya Hajiya Rabi Sule Maiyawo da yara uku Lawal Abubakar, Engr Buhari Abubakar da kuma Engr Mustapha Abubakar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng