An rufe makarantu 67 a jihar Jigawa sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafi jihar

An rufe makarantu 67 a jihar Jigawa sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafi jihar

- Akalla makarantun firamare da na sakandire 67 ne aka rufe su a jihar Jigawa sakamakon ambaliyar ruwa

- Shugaban hukumar SUBEB na jihar, Salisu Zakari ya bayyana cewa makarantu na a kananan hukumomi 9 da ambaliyar ruwan tafi shafa

- Haka zalika ya karyata jita jitar cewa dalibai na karantu a karkashin bishiya ko cikin azuzuwa marasa kyau

Akalla makarantun firamare da na sakandire 67 ne aka rufe su a jihar Jigawa sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafi garuruwa da yawa da ke jihar, wacce tai sanadin mutuwar mutane da dama da janyo asarar dukiya mai tarin yawa.

Shugaban hukumar ilimi bai daya SUBEB na jihar Jigawa, Salisu Zakari ya shaidawa manema labarai cewa makarantun da aka rufe, suna cikin kananan hukumomi 9 da ambaliyar ruwan tafi munana.

Ambaliyar ruwan dai ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 30 daga garuruwa 501, tare da lalata amfani gonaki dama dukiyoyin al'umma, wanda ya tilasta da yawan mazauna garuruwan yin hijira don tsira daga ambaliyar.

KARANTA WANNAN: Ba zan halarci bikin rantsar da Fayemi ba saboda kar yan siyasa su wulakanta ni - Fayose

An rufe makarantu 67 a jihar Jigawa sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafi jihar
An rufe makarantu 67 a jihar Jigawa sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafi jihar
Asali: Twitter

Sai dai Salisu Zakari, ya karyata jita jitar da ke yawo na cewar kashi 50 na dalibai na daukar darasi ne a karkashin bishiya yayin kashi 20 ke koyon karatun a azuzuwa marasa kyau.

"Makarantun da lamarin ya shafa bisa jadawalin kananan hukumominsu, akwai Auyo mai makarantu 20, Jahun na da 5, Kafin Hausa na da 6 sai kuma Kirikisamma na da 7. Haka zalika karamar hukumar Kaugama, Mallam Madori, Miga, Ringim da kuma Taura, na da makarantu 2, 1, 13, 5 da kuma 8."

Shugaban hukumar ta SUBEB ya ce an rufe makarantun ne sakamakon rashin hanyar isa cikinsu, wasu kuma sun lalace gaba daya.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel