Yadda kuka hadu haka zaku fadi tare a 2019 - Martanin Buhari ga Obasanjo da Atiku

Yadda kuka hadu haka zaku fadi tare a 2019 - Martanin Buhari ga Obasanjo da Atiku

- Shugaban kasa Buhari ya yi watsi da hadin guiwar Obasanjo da Atiku a yunkurinsu na kayar da shi a zaben 2019

- A ranar Alhamis ne Atiku da Obasanjo suka gana, inda Obasanjo ya gafartawa Atiku laifukan da ya yi masa a baya

- Fadar shugaban kasa ta ce a lokacin da yayan jam'iyyar PDP ke wannan hadaka, shi kuwa Buhari ta aikin gabansa ya ke

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da goyon bayan da tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ya samu daga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, na zama shugaban kasar Nigeria a babban zaben 2019.

Abubakar, wanda shine babban abokin hamayyar Buhari a babban zabe na 2019, ya ziyarci Obasanjo a yammacin ranar Alhamis, tare da wasu manyan malaman addinin Mulunci da na kirista, da kuma wasu jiga jigan jam'iyyar PDP.

Obasanjo a taron ya ce duk da cewa ba salon tafiyar siyasarsa daya da ta Atiku ba, da kuma matsalolin da ke a tsakaninsu da bai bayyana ba, ya ce ya gafatawa Atiku, sakamakon afuwar da tsohon mataimakin nasa ya nema.

Yadda kuka hadu haka zaku fadi tare a 2019 - Martanin Buhari ga Obasanjo da Atiku
Yadda kuka hadu haka zaku fadi tare a 2019 - Martanin Buhari ga Obasanjo da Atiku
Asali: Facebook

Obasanjo ya ce shirin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga saman mulki abu ne mai wuya, sai dai ya ce Atiku ne ya fi cancantar shugabantar kasar fiye da shugaban kasar mai ci a yanzu, yana mai shan alwashin tallafawa Atiku don ganin ya samu nasara a babban zaben.

KARANTA WANNAN: Ba zan halarci bikin rantsar da Fayemi ba saboda kar yan siyasa su wulakanta ni - Fayose

Sai dai, da ya ke jawabi ta bakin Garba Shehu, shugaban kasa Buhari ya sha alwashin kawar da kansa daga hadakar abokan hamayyarsa don cimma na shi muradin.

"Fadar shugaban kasa ta samu labarin yadda tsohon Shugabankasa Olusegun Obasanjo ya yi amai a baya yanzu kuma ya lashe, na marawa dan takarar shugaban kasa karkashin PDP baya, a wata ganawa da Atiku ya yi da shi a ranar Alhamis, hakika muna matukar mamaki da wannan ribas da Obasanjo ya yi," a cewar sanarwar.

"Yadda suka hada kansu, haka zasu fadi tare. Jin bayanan da tsohon shugaban kasar ya gabatar a wajen ganawar ya bayyana irin halayensa karara na cewar shi ya fi kowa sanin komai."

Sanarwar ta ce a lokacin da yan jam'iyyar PDP ke kulla tuggun kawar da Buhari daga mulki, shi kuwa shugaban kasar ya mayar da hankalinsa ne wajen farfado da tattalin arzikin kasar, kawo karshen rikice rikice, yaki da cin hanci da rashawa, kara samar da wutar lantarki, bunkasa ilimi da bangaren kiwon lafiya, da kuma samar da ayyukan more rayuwar kamarsu tituna, layin dogo, tashar jiragen sama da sauransu.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.naija.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel