An kama wani kasurgumin barawo sanye da kakin sojoji a Najeriya

An kama wani kasurgumin barawo sanye da kakin sojoji a Najeriya

Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Ogun dake a yankin Kudu maso yammacin Najeriya sun samu nasarar cafke wani mutum da ake zargin kasurgumin barawo ne da kan sanya kayan sojoji tare da kwacewa jama'a kudaden su a Karamar hukumar Obafemi-Owode.

Barawon dai wanda aka ce shekarun sa kwata-kwata 23 an kama shi ne wajen karfe 8 na dare jim kadan bayan da ya kwatar wa wani tsohon soja mai suna Adeyemo Adegboyega Naira 86,000 a tsakiyar watan nan da muke ciki.

An kama wani kasurgumin barawo sanye da kakin sojoji a Najeriya
An kama wani kasurgumin barawo sanye da kakin sojoji a Najeriya
Asali: UGC

KU KARANTA: Aikin sabuwar matatar mai a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa tsohon sojan ne da hadin gwiwar jami'an 'yan sandan suka bibiyi sawun barawon har kuma suka kama shi inda dubun sa ta cika.

A wani labarin kuma, Hadaddiyar kungiyar nan ta 'yan kabilar yarbawa dake da'awar kare hakkin su da mutuncin su a Najeriya mai suna Afenifere ta yi fata-fata da tsohon gwamnan jihar Legas, kuma jigo a jam'iyyar APC, Cif Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar ta Afenifere tana tsokaci ne akan kalaman da jigon na APC yayi game da takaddamar da ake fama da ita a kasar ta tsakanin fulani da manoma akan wuraren kiwo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel