Amfani da rubabben tumatur na haifar da ciwon daji - NAFDAC ta gargadi jama'a

Amfani da rubabben tumatur na haifar da ciwon daji - NAFDAC ta gargadi jama'a

- NAFDAC ta gargadi yan Nigeria kan amfani da rubabbun tumatur

- Hukumar ta ce akwai kwayoyin sinadaran da ke iya haddasa ciwon daji a jikin tattare da shi

- NAFDAC ta shawarci 'yan Nigeria da su kauracewa sayen rubabben tumatur kawai saboda arha

Hukumar da ke lura da harkokin tsaftace abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, ta gargadi 'yan Nigeria daga amfani da rubabben tumatur, don gujewa kamuwa daga cutar ciwon daji.

Christiana Essenwa, mataimakiyar daraktan hukumar, ta yi wannan gargadi a cikin watan zantawa da manema labarai a Onitsa, cibiyar kasuwancin jihar Anambra.

A cewarta, rubabbun tumatur na dauke da kwayoyin sinadaren da ke haifar da ciwon daji a jikin dan Adam.

KARANTA WANNAN: Kotu ta tabbatar da Uzodinma a matsayin dan takarar gwamnan Imo karkashin APC

Amfani da rubabben tumatur na haifar da ciwon daji - NAFDAC ta gargadi jama'a
Amfani da rubabben tumatur na haifar da ciwon daji - NAFDAC ta gargadi jama'a
Asali: Facebook

Essenwa ca ce da yawan mutane na tunanin cewa rubabbun tumutu na da arhar saye, kuma za su iya amfani da shi da zaran sun wanke ko sun dafa shi, tana mai cewa kwayoyin cutar da ke jikinsa basu mutuwa koda kuwa an wanke ne ko an dafa shi, kasancewar zafi baya aiki a jikinsu.

Don haka Essenwa, ta shawarci yan Nigeria da su kauracewa rubabbun tumatur kwata-kwata komai arharsu a kasuwa, don kare lafiyarsu daga kamuwa daga cutar ciwon daji.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel