Zanga zangar 'yan Shi'a a Abuja: Sun bukaci 'yan Nigeria su maida Buhari Daura a 2019

Zanga zangar 'yan Shi'a a Abuja: Sun bukaci 'yan Nigeria su maida Buhari Daura a 2019

- Yan shi'a sun gudanar da zanga zanga a gaban fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Laraba

- Sun bukaci 'yan Nigeria da su tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019

- Sun gudanar da zanga zangar ne donnjadda bukatarsu ta sakin shugabansu El-Zakzaky

Mambobin mabiya akidar Shi'a a Nigeria INM daga yankin Kudu-maso-Yamma sun bukaci daukacin 'yan Nigeria musamman wadanda ke a shiyyar da su yi amfani da babban zaben 2019 don tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kan shugabancin kasar.

Da yake gabatar da jawabi ga manema labarai a gaban mashigar fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Laraba, Muftahu Zakariyya, kodinetan 'yayan kungiyar na shiyyar Kudu-maso'Yamma, ya ce shugaban kasar bai canci ci gaba da shugabanci ba musamman akan rashin da'ar yin hukunci.

'Yan shi'a dai sun zargi shugaban kasa Buhari da gudanar da mulkin kama karya irin na tsarin soji, suna mai cewa sam baya bin dokokin da kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.

KARANTA WANNAN: Bincike: Citta, Kanwa da Zuma na magance matsalar radadi da yawan zubar jinin al'ada ga mata

Zanga zangar 'yan Shi'a a Abuja: Sun bukaci 'yan Nigeria su maida Buhari Daura a 2019
Zanga zangar 'yan Shi'a a Abuja: Sun bukaci 'yan Nigeria su maida Buhari Daura a 2019
Asali: Twitter

Ko a baya bayan nan dai 'yan Shi'a na ci gaba da gudanar da jerin gwanon zanga zanga a jihohi da dama na kasar, ciki kuwa harda babban birnin tarayya Abuja, inda suke bayyana bukatar sakin shugabansu Ibraheem El-Zakzaky, wanda gwamnati ke tsare da shi tun 2015, duk da cewa kotu ta bayar da umurnin sakinsa.

"Munzo Abuja a yau don kara jaddada bukatarmu na a saki jagoranmu, tare da nusar da gwamnati akan bin umurnin kotu. Kowa yasan kotu ta ce a saki El-Zakzaky tare da biyansa N50m sakamakon barnar da akayi masa na tsare shi ba bisa ka'ida ba, amma gwamnati ta yi kunnen uwar shegu da wannan umurni na kotu. Don haka bai kamata wani Yoruba ya sake zabar Buhari ba," a cewar Muftahu Zakariyya.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: APC na da 'yan takara a jihar Zamfara - Martanin Oshiomhole ga INEC

Muftahu ya yi ikirarin cewa duk dan Nigeria da ya zabi Buhari a 2019, to kamar ya amince da ci gaban kashe kashen da akeyi a jihohin da rikicin 'yan ta'adda yaki ci yaki cinyewa, yana mai cewa Buhari bai damu da bin dokokin da kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar ba.

"Kuna tunanin ya damu da kashe kashen da ake yi a jihohin Zamfara, Filato, Borno, Benue, Birnin Gwari da sauransu? Wannan ne yasa muke so gaba daya 'yan Nigeria su tsige shi a 2019 don ya koma garinsu Daura."

Sai dai an dakatar da masu zanga zangar daga shiga harabar fadar shugaban kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel