Bincike: Citta, Kanwa da Zuma na magance matsalar radadi da yawan zubar jinin al'ada ga mata

Bincike: Citta, Kanwa da Zuma na magance matsalar radadi da yawan zubar jinin al'ada ga mata

- Bincike ya nuna cewa amfani da garin citta na taimakawa mata wajen rage radadin da suke fuskanta yayin jinin al'ada

- Citta na dauke da sinadaren 'Mefenamic da 'Ibuprofen'

- Haka zalika, amfani da Kanwa da ingantacciyar Zuma na taimakawa wajen rage yawan zubar jinin al'ada

Al'ada mai radadi na takurawa mata a kowane wata, wannan ne kusan babban dalilin da ke hana matan zuwa aiki ko shiga sabgogin jama'a da zaran sun fara. Wannan radadin ke tilasta da yawan matan amfani da kwayar kashe radadi, wacce a karshe take zama maras tabuka komai a jikinsu, yayin da a gefe daya kwayar ke da nata illar ga lafiyar dan Adam.

Amma masana kimiyya sun gudanar da bincike mai zurfi, inda suka gano cewa Citta na dauke da wasu sinadarai guda biyu da ke rage radadin jinin al'ada da kusan kasho 80 ga mata masu fuskantar matsalar. Sinadaran 'Mefenamic da 'Ibuprofen' sune mafi dacewa wajen rage radadin al'ada ga mata.

Masana na ganin cewa radadin al'adar da mata ke fuskanta a kowane wata, na iya faruwa tare da nasabar amai da ganin 'jiri/juwa', wanda suka ce citta na magance wadannan alamomin a jikin mace mai al'ada. Haka zalika citta na rage wadannan alamomi ga mata masu dauke da juna biyu ko wadanda aka yiwa aiki.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: APC na da 'yan takara a jihar Zamfara - Martanin Oshiomhole ga INEC

Bincike: Citta, Kanwa da Zuma na magance matsalar radadi da yawan zubar jinin al'ada ga mata
Bincike: Citta, Kanwa da Zuma na magance matsalar radadi da yawan zubar jinin al'ada ga mata
Asali: Getty Images

Sai dai kwararru a fagen kiwon lafiya, sun yi gargadin cewa adadin yawan garin citta da za a iya amfani da shi kada ya haura giram 6 musamman idan mutum na jin yunwa. Sama da girma 6 na garin citta naniya haifar da matsala ga tsarin 'yan ciki. Haka zalika tana iya haifar da nakasu ga jijiyoyi da kuma haddasa rikicewar daukar bayanan jikin dan Adam.

A shekara ta 2014, wani bincike da aka gudanar a kasar Iran ya bayyana cewa amfani da kasa da grim 6 na garin citta na rage radadin al'ada a wata na farko dana biyu; bashi da wani banbanci da sinadarin 'Mefenamic', binciken ya bukaci mata su rinka yin amfani da 250mg na garin citta bayan awa 6-6 da zaran an fara fuskantar radadi.

KARANTA WANNAN: Kotu ta amince da tuhumar shugaban APC na kasa Adam Oshiomhole bisa zargin aikata Zamba

Bincike: Citta, Kanwa da Zuma na magance matsalar radadi da yawan zubar jinin al'ada ga mata
Bincike: Citta, Kanwa da Zuma na magance matsalar radadi da yawan zubar jinin al'ada ga mata
Asali: UGC

A wani karin binciken, masana sun gano cewa citta na rage yawan kwararar jinin al'ada. A shekara ta 2015, an gwada mata 92 da ke fuskantar yawan zubar jinin al'ada, sun samu waraka ta hanyar amfani da citta a cikin watanni biyu na al'adarsu.

A bangare daya kuwa, masana kimiyya sun ce amfani da ingantacciyar zuma, ko sinadarin kanwa, da kuma sinadarin da ke kunshe a jikin kifi, kamar sadin, salmon da sauransu, na taimakawa mata wajen rage radadi da kuma yawan zubar jinin al'ada.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.naija.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel