Da duminisa: PDP na shirin cire surukin Kwankwaso daga matsayin dan takaran gwamnan jihar Kano, Daga majiya

Da duminisa: PDP na shirin cire surukin Kwankwaso daga matsayin dan takaran gwamnan jihar Kano, Daga majiya

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP na shirin maye Abba Yusuf Kabir, da wani a matsayin dan takaran gwamnan jihar Kano a zaben 2019.

Jaridar Daily Nigerian ta tattaro cewa mataimakin shugaban jam'iyyar ta kasa bangaren Arewa maso yammacin Najeriya, Ibrahim Kazaure, ne ke kan gaba wajen wannan sabon shirin bisa ga zargin cewa zaben fidda gwanin da Yusuf Abba ya lashe akwai magudi.

Game da cewar majiya, kimanin deleget 50 da suka kunshi shugabannin jam'iyyar a kananan hukumomi da dattawan jamiyyar zasu hadu a Abuja yau Laraba domin zaben wanda suka ga ya cancanta da maye Abba Yusuf.

Da duminisa: PDP na shirin cire surukin Kwankwaso daga matsayin dan takaran gwamnan jihar Kano, Daga majiya
Da duminisa: PDP na shirin cire surukin Kwankwaso daga matsayin dan takaran gwamnan jihar Kano, Daga majiya
Asali: Facebook

An yi kokarin tuntuban kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbodiyan domin jin na bakinshi amma hakan bai yiwu ba.

Amma wani jigon Kwankwasiyya, Mohammed Diggol, ya nuna rashin amincewarsa ga hakan saboda INEC ta kulla kofan gudanar da zaben fidda gwani kuma duk wata zabe da aka gudanar a wajen jihar Kano ta bogi ce.

KU KARANTA: An fallasa wani gwamna Kano da aka kama yana karbar cin hancin dala miliyan 5

Mun kawo muku rahoton cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na jihar Kano ta gudanar da zaben fitar da gwanin kujerar gwamnan jihar a gidan babban jigon jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

An kaddamar da zaben ne misalin karfe 12 na dare game da rahoton da jaridar Daily Nigerian ta samu. Wannan zaben ne Abba Yusuf ya lashe da kimanin kuri'u 4,130.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel