Kisan Janar a Filato: Kungiyoyin addinai sun rikita garin Jos da zanga-zanga

Kisan Janar a Filato: Kungiyoyin addinai sun rikita garin Jos da zanga-zanga

Yayin da jami'an rundunar sojin Najeriya ke cigaba da neman tsohon jami'in ta Janar Idris Alkali da ya bace tun a watan jiya a garin Jos, wasu kungiyoyin addinai da dama sun gudanar da zanga-zanga a garin Jos game da hakan.

Kungiyoyin dai wadanda suka fito saman titunan na garin Jos, suna rike ne da kwalaye masu dauke da sakwonni da dama a jikin su da ke nuna rashin jin dadin nasu da irin kashe-kashen da mutanen kauyen Dura-Du kauyen ke yi wa mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Kisan Janar a Filato: Kungiyoyin addinai sun rikita garin Jos da zanga-zanga
Kisan Janar a Filato: Kungiyoyin addinai sun rikita garin Jos da zanga-zanga
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsohon Ambasadan Najeriya a Girka ya mutu

Legit.ng ta samu cewa shugaban masu zanga-zangar, mai suna Deacon Rotdunna Sekat ya bayyana cewa ya zama dole gare su da su fito su bayyana rashin jin dadin su game da bakar dabi'ar da wasu kabilun jihar tare kuma da nuna goyon bayan su ga sojojin Najeriya akan aikin nasu.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa har yanzu jami'an tsaro na acan suna neman Janar din wanda aka ce su nemi ko a raye ko a mace.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari a jiya ya roki malaman addinai a Najeriya da su taimaka ma gwamnatin sa wajen ganin ta yi nasa a yakin da take yi da 'yan ta'addan dake boyewa cikin rigar addini.

Shugaban kasar yayi wannan roko ne a lokacin da ya karbin bakuncin shugabannin kungiyar Qdiriyya ta Afrika a karkashin jagorancin shugaban ta Sheikh Qribullah Nasiru Kabara a fadar sa dake a garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel