Kwanaki 2 da nasarar Atiku: Mutane 10,000 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a Niger Delta

Kwanaki 2 da nasarar Atiku: Mutane 10,000 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a Niger Delta

- Freedom Adowei, tare da wasu magoya bayansa 10,000 daga Niger Delta sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

- Wannan sauya shekar ta zokwanaki 2 bayan samun nasarar da Atiku Abubakar yayi na zama dan takarar shugaban kasa karkashin PDP

- Adowei ya ce ya sauya shekar nan duba da irin ayyukan raya kasa da Gwamna Ifeanyi Okowa ya gudanar a jihar

Wani tsohon shugaban kungiyar da ke fafutukar bunkasa yankin Niger Delta, Freedom Adowei, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC, zuwa jam'iyyar PDP, tare da wasu magoya bayansa 10,000 da ke lungu da sakon jihar.

Wannan sauya shekar ta zo ne kwanaki 2 da samun nasarar lashe zaben Atiku Abukar, na zama dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, zaben fitar da gwani na jam'iyyar da ya gudana a garin Fatakwal, jihar Rivers.

Adowei ya ce ya yanke wannan shawarar na barin APC duba da irin nasarorin da gwamnatin Ifeanyi Okowa, musamman na bunkasa yankunan karkara da rayuwar al'umar jihar, yana mai cewa dan majalisa mai wakiltar mazabar Burutu a majalisar wakilan tarayya, Julius Pondi, na gabatar da wakilci nagari ga mazabarsa.

Kwanaki 2 da nasarar Atiku: Mutane 10,000 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a Niger Delta
Kwanaki 2 da nasarar Atiku: Mutane 10,000 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a Niger Delta
Asali: UGC

KARANTA WANNAN: Bashin Albashin da ma'aikata ke bin gwamnatin jihohinsu a cikin watanni 12 na shekarar 2018

Ya ce: "A karkashin Okowa, al'umomin da ke zaune a yankuna taku a fadin jihar na samun kyakkyawar kulawa fiye da gwamnatocin baya, musamman ta yadda yake maido da su birane daga kauyuka.

"Idan har ka zagaya cikin garuruwan, zaka taras da irin ayyukan raya kasada gwamnan ya gudanar da suka shafi gina tituna a garuruwan da ke makwaftaka da tekuna kamar titin Okerenkoko a masarautar Gbaramatu, Warri ta Kudu-maso-Yamma, titin Sokebolou/Obotobo a masarautar Ogulagha, titin kankare na Burutu da dai sauransu.

"Zan tabbatar da cewa na samawa jam'iyyar PDP kuri'u sama da 20,000 a babban zabe na 2019. A yanzu na sauya shekar ne tare da magoya bayana kuma gaba dayanmu zamu bayar da tamu gudunmowar wajen samun nasarar jam'iyyar a matakin jiha dama kasar baki daya.," a cewar sa.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel