Sanatoci 22 da ba zasu koma majalisan dattawa a 2019 ba (Hotuna)

Sanatoci 22 da ba zasu koma majalisan dattawa a 2019 ba (Hotuna)

Yayinda majalisar dattawa ke shirin dawowa yau Talata, 9 ga watan Oktoba 2018 bayan an kammala zabukan fidda gwanin dukkan jam’iyyun siyasa bisa ga umurin hukumar INEC, Legit.ng ta kawo muku sanatoci 22 da ba zasu koma majalisar.

Sanatoci 22 da ba zasu koma majalisan dattawa a 2019 ba (Hotuna)
Sanatoci 22 da ba zasu koma majalisan dattawa a 2019 ba (Hotuna)
Asali: Twitter

Ga jerinsu:

1.Ahmed Yarima

Kamar yadda labarin ya yadu ko ina, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yarima, ya sadaukar da kujerar sanatansa ga gwamnan jihar, AbdulAziz Yari. Majiya ya bayyana cewa gwamnan ya yiwa sanata Yarima alkawarin kujerar minista, Biliyan goma, da kuma baiwa dan uwansa kujeran dan majalisar tarayya.

2. Bukar Abba

Kamar irin ta Yarima, tsohon gwamnan jihar Yobe, Bukar Abba Ibrahim, ya ci girma ya janye takararsa domin gwamnan jihar, Ibrahim Geidam, ya hau.

3.Ben Murray Bruce,

Sanatan da ya shahara da nuna adawa ga shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana niyyar rashin komawansa majalisa bisa ga tsarin da suke bi a jiharsu ta Bayelsa. Sanatan na daga cikin manyan yan siyasan da ke goyon bayan Atiku Abubakar.

4. Abu Ibrahim,

Sanata Abu Ibrahim na daga cikin dattawan Sanatoci da suka dade a majalisa. Bayan shekaru 16, ba zai sake takaran kujeransa

Sanatoci 22 da ba zasu koma majalisan dattawa a 2019 ba (Hotuna)
Sanatoci 22 da ba zasu koma majalisan dattawa a 2019 ba (Hotuna)
Asali: UGC

5. Rafiu Ibrahim

Wannan sanata wanda tsohon dan majalisan wakilai ne kuma yaron shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ba zai koma ba.

Bayan ya fara yakin neman zaben komawa, an umurceshi ya hakura da kujeran saboda gwamnan jihar Kwara, AbdulFatah Ahmed, ya nuna niyyar takara.

6. Abdullahi Sabi,

Sanata Aliyu Sabi ya sha kasa a zaben fidda gwanin jam’iyyar APC a yankinsa na jihar Neja a hannun wani kwamishana. Ya kasance kakakin majalisar dattawan kuma ya yi bakin jini wajen mutane musamman wajen kokarin kare majalisar.

7. David Umaru,

Hakazalika, Sanata David Buhar ya fadi a zaben fitar da gwanin APC a yankinsa na jihar Neja.

8. Mustapha Sani,

9. Umaru Kurfi

Sanata Kurfi daga jihar Katsina ma ya rasa kujerarsa a zaben fidda gwani.

10. Joshua Lidani,

Sanata Lidani mai wakilar Gombe ta kudu ya rasa kujerarsa yayinda yar majalisar wakilai Binta Bello ta kayar da shi

11. Baba Kaka Garbai,

Garbai wanda ya wakilci Borno ta tsakiya ya samu mulkin a sama bayan rasuwan Zannah Bukar wanda ya ci zabe amma ya rasu kafin rantsar da shi.

Sanatoci 22 da ba zasu koma majalisan dattawa a 2019 ba (Hotuna)
Sanatoci 22 da ba zasu koma majalisan dattawa a 2019 ba (Hotuna)
Asali: UGC

A bangare guda akwai wasu yan majalisar da ba zasu dawo majalisar ba saboda sun nemi kujerar gwamnan jihohinsu. Yayinda wasu suka sha kasa, wasu sun samu nasara. Ga jerinsu<

12. Kabiru Garba Marafa (APC, Zamfara, ya fadi),

13. Jerry Husseini (PDP, Plateau, ya ci);

14. Sunny Ogbouji (APC, Ebonyi, ya cci)

15. Magnus Abe (APC, Rivers, ya fadi).

16. John Owan-Enoh (APC, C/River, ya ci);

17. Usman Bayero Nafada (PDP, Gombe, ya ci);

18. Suleiman Hunkuyi (PDP, Kaduna, ya sha kasa);

19. Hope Uzodinma (APC, Imo, ya sha kasa);

20. Abdulaziz Murtala Nyako (ADC, Adamawa, ya ci),

21. Philip Aruwa Gyunka (PDP, Nasarawa, ya fadi);

22. Shaba Lafiagi (PDP, Kwara, ya sha kasa)

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel