Nuhu Ribadu: Babu wata tsiyar da Fulani ke amfana a gwamnatin Buhari

Nuhu Ribadu: Babu wata tsiyar da Fulani ke amfana a gwamnatin Buhari

- Nuhu Ribadu, ya ce Fulani ba sa amfana da wani romon demokaradiyya a Nigeria

- Ribadu ya ce jama'ar Fulani na tunanin cewa Buhari ya yi watsi da sha'anin bunkasa rayuwarsu

- Ya ce sune suke da akalla yawan mutane miliyan 15 zuwa 20 na adadin mutanen Nigeria

Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar dake yaki da yiwa dukiyar al'umma zagon kasa (EFCC), ya ce Fulani ba sa amfana da wani romon demokaradiyya a Nigeria karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ribadu ya ce jama'ar Fulani na tunanin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da sha'anin bunkasa rayuwarsu, wanda ya sa suke fushi da shi a wannan lokaci.

A cewar jaridar The Nation, Ribadu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taro na gano bakin zaren rikicin makiyaya da manoma a kasar.

Nuhu Ribadu ya ce ya zama wajibi Nigeria ta tashi tsaye don shawo kan rikicin makiyaya da manoma, musamman ma ganin cewa sha'anin kiwon dabbobi a kasar ba bakon al'amari bane a kasar.

Nuhu Ribadu: Babu wata tsiyar da Fulani ke amfana a gwamnatin Buhari
Nuhu Ribadu: Babu wata tsiyar da Fulani ke amfana a gwamnatin Buhari
Asali: Twitter

KARANTA WANNAN: Atiku Babban barawo ne a Afrika: Manyan badakaloli biyar da ya tafka - Rahoton Amurka

"Mun manta da cewar mutanen da ke zaune ba tare da muhalli ba za su ci gaba da bullo da matsaloli, kuma daya daga cikin matsalolin da muke fuskanta a yau shine wadannan mutanen da ke cewa suma 'yan kasar ne. Suna son a basu wani bangare na kasar da zai zama mallakinsu, amma hakan ya tayar da tarzoma. Wannan ne kawai babban dalilin rikicin Zamfara, Birnin Gwari da kuma wasu sassa na kasar," a cewar sa.

"Makiyayan da ke zaune a garuruwan da ke ikirarin cewar suma garinsu ne, ko kuma shuwagabanninsu da ke ikirarin sune shuwagabannin garuruwan, sun kasa fahimtar inda suka dosa. Su mutane ne da suka saba da rayuwar mutanen garuruwan da suke son mallaka.

KARANTA WANNAN: Dankwambo ya amince da shan kayi a hannun Atiku: Ya bayyana makomarsa a PDP

"Zai yi matukar wahala ka taras da wani Bafullatani a wata majalisa ta jiha ko ta tarayya, kuma sune suke da akalla yawan mutane miliyan 15 zuwa 20 na adadin mutanen Nigeria, kuma su mutane ne da aka waresu daga dukkanin sha'anonin shugabancin kasar."

Ribadu ya kara da cewa Nigeria bata da wani yunkuri na bunkasa rayuwar Fulani a kasar, idan aka cire ilimin makiyaya da ake yi a kasar, babu wani shirin bunkasa rayuwarsu da ake yi don suma su zamo masu bada gudunmowa wajen ci gaban kasar.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel