Kamanceceniya 5 dake a tsakanin Shugaba Buhari da Atiku

Kamanceceniya 5 dake a tsakanin Shugaba Buhari da Atiku

A jiya ne dai taron gangamin babbar jam'iyyar adawa ta PDP da aka dade ana tsumaye ya zo karshe inda kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma fitaccen dan siyasar nan Atiku Abubakar ya samu nasarar samun tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyyar ta PDP.

Atiku Abubakar din dai ya kayar da sauran abokan takarar sa ne da babban rinjaye a zaben da aka shafe sama da kwana daya ana yi a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Kamanceceniya 5 dake a tsakanin Shugaba Buhari da Atiku
Kamanceceniya 5 dake a tsakanin Shugaba Buhari da Atiku
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sarki Sanusi ya soki salon mulkin Shugaba Buhari a kaikaice

Wannan dai na nuni da cewa zaben shekarar 2019 zai kasance ne a tsakanin manyan 'yan takarar shugabancin kasar nan guda biyu - watau shi Atiku Abubakar din daga PDP, sai kuma Shugaba Muhammadu Buhari daga APC.

Ga dai wasu kamanceceniyar dake tsakanin mutanen biyu da muka zakulo maku.

1. Yare ko kabila

Dukkan mutanen biyu dai watau shi Atiku Abubakar din daga PDP, sai kuma Shugaba Muhammadu Buhari daga APC 'yan kabilar Fulani ne kuma suna jin Hausa rangadakau.

2. Shekaru

Dukkan fitattun 'yan siyasar da za su fafata a zaben na 2019 dai sun haurawa shekaru 70 a duniya. Yayin da shugaba Buhari zai cika shekaru 75, shi kuwa Atiku zai cika shekaru 73 ne.

3. Aikin khaki

Kamanceceniya 5 dake a tsakanin Shugaba Buhari da Atiku
Kamanceceniya 5 dake a tsakanin Shugaba Buhari da Atiku
Asali: Depositphotos

Shugaba Muhammadu Buhari dai tsohon soja ne shi kuma Atiku Abubakar, tsohon jami'in kwastam be. Su duka sun yi aikin khaki.

4. Yankin da suka fito

Su duka 'yan takarar dai sun fito ne daga yankin Arewacin Najeriya. Atiku Abubakar ya fito ne daga jihar Adamawa yayin da shi kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya fito daga jihar Katsina.

5. Marayu ne

Haka zalika shi Atiku Abubakar din daga PDP da kuma Shugaba Muhammadu Buhari daga APC dukkan su marayu ne domin kuwa iyayen su duk sun rasu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel