Ba-kunya-ba-tsoron-Allah: Yadda kyamarar boye ta fallasa gwamnan Arewa yana karbar cin hanci

Ba-kunya-ba-tsoron-Allah: Yadda kyamarar boye ta fallasa gwamnan Arewa yana karbar cin hanci

- Kyamarar boye ta fallasa gwamnan Arewa yana karbar cin hanci

- Gwamnan dai ya fito ne daga Arewa maso gabashin Najeriya

- Gwamnan kuma yana neman tazarce yanzu haka a APC

Daya daga cikin gwamnoni shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya ya tsoma kan shi cikin cakwakiya biyo bayan wani faifan bidiyon sa da wata kyamarar boye ta dauka yana karbar cin hanci daga 'yan kwangila daban-daban.

Ba-kunya-ba-tsoron-Allah: Yadda kyamarar boye ta fallasa gwamnan Arewa yana karbar cin hanci
Ba-kunya-ba-tsoron-Allah: Yadda kyamarar boye ta fallasa gwamnan Arewa yana karbar cin hanci
Asali: Facebook

KU KARANTA: Mabanbantan ra'ayoyin 'yan Najeriya game da takarar Atiku da Buhari

Kamar dai yadda majiyar mu ta Daily Nigerian ta ruwaito, gwamnan wanda dan jam'iyyar APC ne kuma yanzu haka yake neman sake zarcewa a karo na biyu, ana tunanin wannan aikin asshan da ya tafka na iya kawo masa tarnaki.

Legit.ng ta samu cewa faya-fayan bidiyon dai wadanda suka fita a bainar jama'a sun kai guda uku wadanda a ciki kuma aka samu cewa kudaden cin hancin da ya karba jumillar su ta kai dalar Amurka miliyan 5.

Duk da dai majiyar ta mu bata fada mana wane gwamnan bane, amma dai shiyyar Arewa maso yamma tana da jahohi 7 kuma dukkan su 'yan APC ne banda jihar Sokoto.

Haka zalika yayin da duka gwamnonin ke neman tazarce bayan cikar wa'adin mulkin su na farko, gwamnan jihar Zamfara shi wa'adin mulki na biyu ne yake yi yanzu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel