Za mu tsige Saraki idan majalisar dokoki ta dawo – Shugaban masu rinjaye a majalisa ya sha alwashi

Za mu tsige Saraki idan majalisar dokoki ta dawo – Shugaban masu rinjaye a majalisa ya sha alwashi

- Shugaban masu rinjaye a majalisa yace za su yi duk abunda za su iya da karfin su don tabbatar da tsige Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

- Lawan yace da zaran majalisar dokokin kasar ta dawo zama, shi da sauran yan APC zasu tabbatar da cewa an maye wa gurbin Saraki da wani

- Ya kuma ce za su aiwatar da kasafin kudin zabe da na hukumomin tsaro

Shugaban masu rinjaye a majalisa, Ahmed Lawan, ya ba jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tabbacin cewa sanatocin jam’iyyar za su yi duk abunda za su iya da karfin su don tabbatar da tsige Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

Lawan yace da zaran majalisar dokokin kasar ta dawo zama, shi da sauran yan APC zasu tabbatar da cewa an maye wa gurbin Saraki da wani sannan kuma a aiwatar da kasafin kudin zabe da na hukumomin tsaro.

Za mu tsige Saraki idan majalisar dokoki ta dawo – Shugaban masu rinjaye a majalisa ya sha alwashi
Za mu tsige Saraki idan majalisar dokoki ta dawo – Shugaban masu rinjaye a majalisa ya sha alwashi
Asali: UGC

Lawan ya bayyana hakan a babban taron APC na kasa da aka gudanar a karshen mako, jaridar The Sun ta ruwaito.

A cewarsa za su koma majalisa a ranar Talata inda zasu gudanar da muhimman ayyukan da suka kamata.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa kasa da sa’o’i shida bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi nasarar zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, wata gamayyar jam’iyyun siyasa 39 sun kaddamar da shirinsu na daukarsa a matsayin dan takarar shugaban kasa na hadin gwiwa.

KU KARANTA KUMA: Surukin Gwamnan Imo Uche Nwosu ya samu tikitin takara a Jam’iyyar APC

Jam’iyyun karkashin lemar Coalition of United Political Parties (CUPP), wanda PDP ke jagoranta sunce zasu dinke da shi a matsayin dan takarar hadin gwiwa a zaben saboda suyi waje da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel