Da dumin sa: Aisha Buhari tayi kaca-kaca da shugaban jam'iyyar APC, Oshiomhole

Da dumin sa: Aisha Buhari tayi kaca-kaca da shugaban jam'iyyar APC, Oshiomhole

- Aisha Buhari tayi kaca-kaca da shugaban jam'iyyar APC, Oshiomhole

- Daman dai ta taba sukar jam'iyyar ta APC a 2016

- Yanzu kuma tace shugaban ta na shirin rusa ta

Uwar gidan shugaban kasar tarayyar Najeriya, Aisha Buhari ta fito fili ta nuna rashin jin dadin ta game da yadda jam'iyyar su ta APC ta gudanar da zabukan fitar da gwani a dukkan matakai a karkashin jagorancin Adams Oshiomhole.

Da dumin sa: Aisha Buhari tayi kaca-kaca da shugaban jam'iyyar APC, Oshiomhole
Da dumin sa: Aisha Buhari tayi kaca-kaca da shugaban jam'iyyar APC, Oshiomhole
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Atiku ya kama hanyar lashe zaben PDP

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a wani lokaci can cikin shekarar 2016 Aisha Buhari din ta fito fili ta soki mijin na ta da kuma jam'iyyar sa inda tace idan harkokin jam'iyyar suka cigaba da tafiya a hakan to fa tabbas ba zata mara mata baya ba a 2019.

Legit.ng dai ta samu cewa kalaman na ta na kwanan nan ba su rasa nasaba da rashin nasarar da kanin ta yayi a zaben fitar da gwani na jam'iyar a jihar Adamawa da yayi takarar gwamna.

A wani labarin kuma, A shekarar 2015, jim kadan bayan da aka sanar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben da aka gudanar, wani abun da ya dauki hankalin al'umma shine tattakin da wani matashi yayi daga jihar Legas zuwa Abuja.

Matashin mai suna Suleiman Hashim, a lokacin ya ce yana yin tattakin ne domin taya shugaba Buhari murnan lashe zabe da kuma yiwa 'yan Najeriya murna su ma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel