Al'ajabi: Wakilan APC 6 sun mutu jim kadan bayan jefa kuri'arsu a Jigawa

Al'ajabi: Wakilan APC 6 sun mutu jim kadan bayan jefa kuri'arsu a Jigawa

- Wakilan jam'iyyar APC 6 sun mutu jim kadan bayan jefa kuri'arsu a zaben fitar da gwani na jihar Jigawa

- Rundunar 'yan sanda ta ce wakilan sun mutu ne a hatsarin mota da ya rutsa da su sakamakon gudu mai tsanani

- Gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya mika sakon ta'aziyyarsa na mutuwar wakilan

Jam'iyyar APC ta rasa wasu wakilai masu jefa kuri'a a zaben fitar da gwani daga mazabar mazabar Arewa-maso-Gabas a jihar Jigawa. Wakilan sun mutu ne awanni kadan da jefa kuri'arsu a zaben fitar da gwani na kujerar Sanatan mazabar Jigawa ta Arewa-maso-Gabas.

Mummunan hatsarin mota ne ya zama silar mutuwar wakilan, bayan da suka je karamar hukumar Gumel don jefa kuri'arsu, a hanyarsu ta komawa karamar hukumarsu, Guaiwa, bayan jefa kuri'asu da misalin karfe goma da rabi na yammacin Juma'a.

Da ya ke tabbar da faruwar wannan mummunar hatsarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Jigawa, SP Abdul Jinjiri, ya ce, "hadarin ya auku a wani kauye da ke kan hanyar Gumel zuwa Babura mai suna Dantado. Hatsarin ya rutsa da karamar mota kirar Gulf 3 tare da wata mota kirar bas mai lamba, DB 421 KZR."

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan bangar siyasa 100 dauke da muggan makamai a Kebbi

Al'ajabi: Wakilan APC 6 sun mutu jim kadan bayan kada kuri'arsu a zaben a Jigawa
Al'ajabi: Wakilan APC 6 sun mutu jim kadan bayan kada kuri'arsu a zaben a Jigawa
Asali: Twitter

SP Jinjir ya labarta yadda hatsarin ya auku da cewar, "Su duka motocin na dauke da wakilan jam'iyyar APC da suka jefa kuri'a a karamar hukumar Gumel, suna kan hanyar komawarsu Guaiwa. Kasancewar suna matsanancin gudu, a lokacin da direban bas din ya yi kokarin wuce karamar motar, sai suka gogi juna, hakan ya sa motar ta kwacewa direban.

"Motar na kwacewa sai suka afka daji, wannan yasa motar bas din jujjuyawa tana wulkitawa har dai ta kashe mutanen da ke ciki gaba dayansu har da matukin motar, a nan take."

Da ya ke mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka mutu dama jihar Jigawa, gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar, ya ce ya kadu matuka da jin labarin mutuwarsu.

Ya ce, mamatan sun ketare duk wahalhalu suka zo Gumel domin cin moriyan ‘yancin su, su kuma sauke nauyin da ke hansu a matsayin su na wakilai, domin su zabi shugabannin da za su jagoranci kasa.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel