Batan-baka-tan-tan: Akwai yiwuwar APC ta rasa dan takara a wata jihar Arewa a zaben 2019

Batan-baka-tan-tan: Akwai yiwuwar APC ta rasa dan takara a wata jihar Arewa a zaben 2019

- Akwai yiwuwar APC ta rasa dan takara a wata jihar Arewa a zaben 2019

- Sanata Marafa daga jihar Zamfara ne ya fadi hakan

- Zaben fitar da gwani na APC a jihar ta Zamfara na fuskantar matsaloli sosai

Daya daga cikin masu neman tikitin takarar gwamna a jam'iyyar APC a jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya kuma Sanatan dake wakiltar mazabar jihar ta Zamfara ta tsakiya, Sanata Kabiru Marafa ya ce akwai yiwuwar jam'iyyar su ta APC ta rasa dan takarar gwamna a jihar a zaben 2019 mai zuwa.

Batan-baka-tan-tan: Akwai yiwuwar APC ta rasa dan takara a wata jihar Arewa a zaben 2019
Batan-baka-tan-tan: Akwai yiwuwar APC ta rasa dan takara a wata jihar Arewa a zaben 2019
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zaben fitar da gwanin PDP:

Sanata Marafa ya bayyana cewa idan dai har uwar jam'iyyar ta kasa ta kasa gudanar da sahihin zabe kafin kurewar lokaci na ranar Lahadi, 7 ga watan Oktoba, to fa lallai ne jam'iyyar ta shirya shiga zabukan na 2019 ba tare da dan takara ba.

Legit.ng ta samu cewa wannan dai na zuwa ne bayan uwar jam'iyyar ta soke zabukan fitar da gwanin da aka fara a jihar ranar Alhamis din da ta gabata sannan kuma ta rushe dukkan zababbun shugabannin jam'iyyar a matakin jihar ranar Juma'a.

A wani labarin kuma, A wani zaben gwaji a dandalin sada zumuntar zamani na Tuwita, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe wani dan kwarya-kwaryan zaben fitar da gwani na gwaji da aka gudanar.

A zaben wanda akawunt din jam'iyyar PDP na jihar Ribas ya gudanar, Atiku Abubakar din ya sanmu mafiya yawan kuri'un da aka kada inda ya kada shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Sanata Kwankwaso da kuma Aminu Tambuwal.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel