APC: Sunayen yan takarar majalisar tarayya da suka lashe zaben fidda gwani na jihar Jigawa

APC: Sunayen yan takarar majalisar tarayya da suka lashe zaben fidda gwani na jihar Jigawa

- APC ta bayyana sunayen yan takarar kujerar majalisar wakilan tarayya daga jihar Jigawa bayan kammala zaben fidda gwani

- Sai dai ba a gudanar da zabe a mazabar Gwaram ba

- Haka zalika gaba daya yan majalisu masu ci a yanzu sun sake lashe zabe banda Sani Zoro da Mohammed Gausau Boyi

An gudanar da zaben fitar da gwani na kujerun majalisun wakilai na tarayya karkashin jam'iyyar APC cikin lumana a gaba daya mazabu 11 na jihar Jigawa. Mazabar Gwaram ne kadai ba a gudanar da zaben ba, wanda har zuwa yanzu babu wani dalili da jam'iyyar ta bayar.

Gaba daya yan majalisun tarayyar masu ci a yanzu, sun sake lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar, sai dai banda Sani Zoro da Mohammed Gausau Boyi. Sani Zoro dai ya taba rike mukamin shugaban kungiyar yan jarida ta kasa NUJ.

Ga dai wadanda suka lashe zaben fitar da gwanin, wadanda za su tsaya takara a zaben 2019 karkashin jam'iyyar APC don wakiltar mazabunsu a majalisar wakilai ta tarayya.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Gwamnonin PDP sun rantse ba zasu goyi bayan kowanne dan takara ba

APC: Sunayen yan takarar majalisar tarayya da suka lashe zaben fidda gwani na jihar Jigawa
APC: Sunayen yan takarar majalisar tarayya da suka lashe zaben fidda gwani na jihar Jigawa
Asali: UGC

A mazabar Birniwa/Kirikisamma/Guri, Abubakar Hassan Fulata ya lashe zaben fitar da gwanin da kuri'u 648, Mohammed Gudaji Danbappah, ya lashe zaben mazabar Kazaure/Roni/Yankwashe/Gwiwa da kuri'u 693.

Engineer Magaji Da’u Aliyu, shi ne ya daga tutar jam'iyyar a mazabar Birnin kudu/Buji bayan samun kuri'u 366 votes yayin da a mazabar Mallam Madori/Kaugama, Maki Abubakar Yelleman ya samu nasara da kuri'u 302.

Nazifi Sani Gumel, ya doke dan majalisa mai ci a yanzu Sani Zoro, bayan samun kuri'u 550 a mazabar Gumel/Gagarawa/Maigatari/ Suletankarkar, sai kuma a mazabar Miga/Jahu federal, Sa’idu Yusuf Miga, ya lashe zaben fitar da gwanin da kuri'u 717.

KARANTA WANNAN: Kotu ta yanke hukuncin kisa akan direban da ya kashe wani jami'in hukumar FRSC

APC: Sunayen yan takarar majalisar tarayya da suka lashe zaben fidda gwani na jihar Jigawa
APC: Sunayen yan takarar majalisar tarayya da suka lashe zaben fidda gwani na jihar Jigawa
Asali: Depositphotos

Mohammed Adamu Fagen-Gawo shine ya ciri tutar jam'iyyar ta APC a mazabar Garki/Babura bayan samun kuri'u 277 yayinda shi Usman Ibrahim Company, ya lashe zaben da aka gudanar a mazabarsa ta Kafin Hausa/Hadejia/Auyo da tsereyar kuri'u 497.

A mazabar Dutse/Kiyawa kuwa, Ibrahim Kemba Madobi ya tabbata dan takarar jam'iyyar sakamakon samun kuri'u 413. A bangare daya kuwa, shugaban jam'iyyar na jihar, Ado Sani Kiri ya doke dan majalisa mai ci, Mohammed Gausu Boyi a mazabar Ringim/Taura federal da jimillar kuri'u 501.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel