Yanzu Yanzu: Jimi Agbaje ya yi nasarar samun tikitin PDP a Lagas
Jimi Agbaje ya lashe zaben fidda gwanin gwamna da aka yi a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Lagas a ranar Juma’a, 5 ga watan Oktoba.
Agbaje ya kayar da abokin adawarsa, Deji Doherty da kuri’u 1,100 zuwa 741 jaridar The Cable ta ruwaito.

Asali: Depositphotos
Zaben fidda gwanin wanda ya kwashe tsawon kwanaki biyu ya samu kula daga kwamitin zabe karkashin jagorancin Victor Kassim Oyofo.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da Anyim
A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na fuskantar matsin lamba kan cewa ya hakura da kudirinsa na takarar kujeran shugaban kasa sannan ya marawa Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa baya don ganin ya samu tikitin takarar shugabancin kasa na PDP.
A cewar wani shafin yanar gizo, Sahara Reporters, wata majiya na daya daga cikin makusantar ýan takaran ya bayyana cewa Atiku na ta tattaunawa da sauran yan takara irin su Saraki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng