Rikici da harbe-harbe sun kaure a zaben fidda gwanin yan takarar sanata na PDP a Benue

Rikici da harbe-harbe sun kaure a zaben fidda gwanin yan takarar sanata na PDP a Benue

Rikici ya kaure a zaben fidda gwanin jam’yyar Peoples Democratic Party (PDP) a Makurdi, inda ake ta harbe-harbe wanda yayi saadiyar da mutane 10 suka jikkata, jaridar The Punch ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa a daren ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba, mutane da dama sun ji muggan rauni, inda aka lalata motoci 20 a lokacin zaben fidda gwani na sanata a yankin Benue ta Kudu wanda aka gudanar a Aper Aku Stadium a Makurdi.

An tattaro cewa yan iska sun mamaye mashigin taron zaben fidda gwanin na ýan majaalisun dokokin jihad a na tarayya a yankin Benue ta Kudu.

Zaben fidda gwanin PDP bai yiwu da wuri ba a Otukpo, hedkwatar mazabar, kwamitin zaben sun dage wajen taron zuwa Makurdi don guje ma rikicin.

Rikici da harbe-harbe sun kaure a zaben fidda gwanin yan takarar sanata na PDP a Benue
Rikici da harbe-harbe sun kaure a zaben fidda gwanin yan takarar sanata na PDP a Benue
Asali: Depositphotos

Amma sai gashi rikici ya soma lokacin da wakilan suka ke tantance masu zaben indaa wasu mutane suka yi zanga-zanga akan jerin wakilai daga karamar hukumar Ohimini.

Daga bayane wasu mutane da ake ganin yan daba masu yiwa yan takarar aiki ne suka fara jifann wakilan inda hakan ya tursasa jami’an tsaro harbi a sama domin tarwatsa jama’ar.

KU KARANTA KUMA: Saraki na fuskantar matsin lamba kan cewa ya janye ma Atiku

Amma duk kokarin da yan sanda suka yi, sai wasu ya daba wanda mafi akasarinsu dauke suke da makamai, suka da harbe-harben bindiga, inda hakan ya kai ga rikici.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel