Zaben fitar da gwani: Tambuwal ya samu kwarin gwaiwa daga wani tsohon shugaban kasa

Zaben fitar da gwani: Tambuwal ya samu kwarin gwaiwa daga wani tsohon shugaban kasa

Tsohon shugaban kasar Najeriya a zamanin mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce yana goyon bayan takarar shugancin kasar Najeriya da Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal keyi.

Babangida ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin tsohon kakakin majalisar wakilai ta Najeriya din a gidan sa dake a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Zaben fitar da gwani: Tambuwal ya samu kwarin gwaiwa daga wani tsohon shugaban kasa
Zaben fitar da gwani: Tambuwal ya samu kwarin gwaiwa daga wani tsohon shugaban kasa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe wani babban malamin addini a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa a lokacin ziyarar gwamnan na Sokoto, an tsinkayi tsohon shugaban kasar yana ta zunduma masa albarka tare da yaba masa musamman ma a wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.

Haka zalika ya yaba wa matashin kuma gogaggen dan siyasar akan kokarin da yake yi wajen tabbatar da hadin kan Najeriya ba tare da la'akari da addinance ko kabilanci ba.

A wani labarin kuma, A wani zaben gwaji a dandalin sada zumuntar zamani na Tuwita, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe wani dan kwarya-kwaryan zaben fitar da gwani na gwaji da aka gudanar.

A zaben wanda akawunt din jam'iyyar PDP na jihar Ribas ya gudanar, Atiku Abubakar din ya sanmu mafiya yawan kuri'un da aka kada inda ya kada shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Sanata Kwankwaso da kuma Aminu Tambuwal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel