Tsugune bata kare ba: Kotu ta sake daukar wani mataki akan shari'ar Maryam Sanda dake gabanta
- Kotu ta sake daukar wani mataki akan shari'ar Maryam Sanda dake gabanta
- Kotu ta dage shari'ar zuwa 24 ga watan Oktoba
Shari'ar da wata kutu a garin Abuja ke yi akan Maryam Sanda - matar nan da ta kashe mijin ta a lokutan baya ta dauki wani sabon salo biyo bayan janyewar lauyoyin ta 3 dake kare ta daga shari'ar, kamar dai yadda muka samu daga majiyar mi.

Asali: UGC
KU KARANTA: An kai wa Ado Gwanja farmaki a ofishin sa
Biyo bayan hakan ne kuma, haka zalika sai kotun ta sake daga shari'ar da take yi akan karar da aka shigar mata ya zuwa 24 ga watan Oktoba domin cigaba.
Legit.ng dai ta samu cewa Maryam Sanda ana tuhumar ta ne da kisan mijin ta mai suna Bello, da ga tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Alhaji Halliru Bello.
A tare da ita Maryam din wajen tuhuma, hadda kanin ta Aliyu, sai mamar ta Maimuna da kuma kawar ta Sa'adiyya wadanda aka ce sun taimaka mata wajen boye shaidu.
A wani labarin kuma, Hukumar rundunar sojojin Najeriya ta yi tayin kyautar makudan kudade ga dukkan wanda ya taimaka mata da muhimman bayanan da za su taimaka mata a cigaba da neman Janar Idris Alkali da take yi a karamar hukumar Jos ta kudu, jihar Filato.
Bataliya ta 3 ta rundinar dake kula da shiyyar jihar ta Filato ce dai ta bayar da sanarwar hakan tare kuma da kara jaddada kudurin su na tabbtar da sun gano Janar din wanda ya bace a raye ko a mace.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng