Cikin wata 1: Hukumar kwastam ta cafke motoci 22 da kudinsu ya kai N2bn

Cikin wata 1: Hukumar kwastam ta cafke motoci 22 da kudinsu ya kai N2bn

- Hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam), ta ce ta samu nasarar cafke kayayyaki daban daban da suka kai darajar Naira biliyan biyu

- A cewar hukumar, sun samu nasarar cafke kayayyakin ne daga 4 ga watan Satumba zuwa 3 ga watan Oktoba

- Daga cikin kayayyakin akwai motoci guda 22 wadanda keda garkuwa daga harsashen bindiga, da kudinsu ya kai N1.179bn

Hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam), sashen 'Zone A' na gwamnatin tarayya, a ranar Alhamis, hukumar ta ce ta samu nasarar cafke kayayyaki daban daban wadanda ba su da takardar DPV da suka kai darajar Naira biliyan biyu.

Daga cikin kayayyakin da aka kama akwai motoci guda 22 wadanda keda garkuwa daga harsashen bindiga, da kudinsu ya kai N1.179bn.

Hukumar ta ce a sa'ilin da aka cafke wasu motocim a Ogere da Ijebu Ode, an kuma gano wasu motocin da dama a wani gida dake kan tsibirin Victoria, jihar Legas.

A cewar hukumar, sun samu nasarar cafke kayayyakin ne daga 4 ga watan Satumba zuwa 3 ga watan Oktoba.

KARANTA WANNAN: PDP na zargin APC da yunkurin dakatar da ita daga gudanar da babban taronta na kasa

Cikin wata 1: Hukumar kwastam ta cafke motoci 22 da kudinsu ya kai N2bn
Cikin wata 1: Hukumar kwastam ta cafke motoci 22 da kudinsu ya kai N2bn
Asali: Original

Kwanturola Mohammed Alitu, kwanturolan rundunar na yankin wanda ya bayyana nakan a ranar Alhamis a Legas, a wani taron manema labarai, ya ce wasu daga cikin kayayyakin da hukumar ta kwace sun hada da motocin alfarma guda 22, wasunsu ma na da garkuwa daga harsashen bindiga.

"Buhunan shinkafa yar kasar waje guda 11,303, da za su kai tirela 1i, katan 2410 na daskararrun kaji da kifi, jarka 853 na man gyada, dila 245 ta tabar wiwi, da dai sauransu."

Mohammed ya ce rundunar ta samu nasarar cafke motocin ne a wani daji da ke cikin Idiroko, cikin jihar zogun, ya yin da aka cafke wasu a cikin wasu shagunan sayar da motoci a Legas.

Ya sha alwashin cewa sashen rundunar na musamman zai ci gaba da farautar masu fasa kwabri da ke harkallolinsu a yankin Kudu maso Yamma, ta hanyar cafke su da kama kayan da suka shigo da su.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel