Da dumin sa: Sabbin bayanai akan neman Janar Alkali da ake yi daga rundunar sojojin Najeriya

Da dumin sa: Sabbin bayanai akan neman Janar Alkali da ake yi daga rundunar sojojin Najeriya

Da yammacin yau ne dai rundunar sojojin Najeriya suka fitar da sanarwa dauke da wasu muhimman bayanai game da cigaba da neman Janar din nan Idris Alkali wanda ya bata a watan Satumban da ya gabata.

Sanarwar wadda take dauke da sa hannun Kanal Kayode Ogunsanya dake zaman mataimakin Darakta a hukumar rundunar mai kula da harkokin hulda da jama'a ta bayyana cewa rahoton da ke yawo a kafafen sadarwar zamani na cewa sojojin sun gano motoci 11 da gawarwakin mutane 2 ba gaskiya bane.

Da dumin sa: Sabbin bayanai akan neman Janar Alkali da ake yi daga rundunar sojojin Najeriya
Da dumin sa: Sabbin bayanai akan neman Janar Alkali da ake yi daga rundunar sojojin Najeriya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buhari ya aikawa Saraki da wata muhimmiyar wasika

Sanarwar ta cigaba da cewa su motoci 3 ne suka samu a cigaba da tsotse ruwan kududdufin garin Dura Du da suke yi amma basu samu gawar mutum ko daya ba. Haka zalika sun bayyana cewa sun samu kayan sawa na Janar din.

Sanarwar ta kara da cewa har yanzu suna nan suna neman Janar din kuma tuni jami'an su suka bazama cikin daji suna neman sa ko da rai ko gawar sa.

Daga karshe ne kuma sai ya shawarci al'umma da su guji bibiyar shafukan da ke yada labaran karya sannan kuma su cigaba da bibiyar kafofin watsa labarai masu sahihanci daga rundunar domin samun labaran cigaban da ake samu game da binciken.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel