Zaben fitar da gwani: 'Yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka

Zaben fitar da gwani: 'Yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka

- 'Yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka

- Suna yi ne domin samun nasarar jagoran su

Yayin da zabukan fitar da gwani don tunkarar zaben shekarar 2019 ke ta kara karatowa, wasu masoyan dan takarar shugabancin kasar dake neman tikitin tsayawa a jam'iyyar adawa ta PDP, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso sun yanka rago tare da addu'o'i ga Allah akan muradin na su.

Zaben fitar da gwani: 'Yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka
Zaben fitar da gwani: 'Yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Gwamnoni 4 sun daura damarar yaki da Oshiomhole

Kamar yadda muka samu, masoyan na Kwankwaso da galibin su matasa ne sun fito ne daga karamar hukumar Kiru dake a jihar Kano inda kuma suka gudanar da Sallah da saukar al'qur'ani duk domin samun nasarar gwanin nasu.

Legit.ng dai ta samu cewa Kwankwaso dake zaman tsohon gwamnan jihar Kano ya fice daga jam'iyyar sa ta APC zuwa PDP a watannin baya inda kuma ya bayyana kudurin sa na tsayawa takara da Shugaba Buhari a watan da ya gabata.

A wani labarin kuma, Akalla gwamnoni hudu ne kawo yanzu suka fito fili suka wasa wukar su domin shiga yaki gadan-gadan da shugaban jam'iyya mai mulki ta APC, Kwamared Adams Oshiomhole game da zabukar fitar da gwani da ake yi yanzu haka.

Gwamnonin da muka samu labarin sun soma yin fito-na-fito da shugaban jam'iyyar dai sune Abdulaziz Yari na jihar Zamfara; Rotimi Akeredolu na jihar Ondo; Nasir El-Rufai daga Kaduna da kuma Ibikunle Amosun daga jihar Ogun.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel